Sai ki na da kuɗi za ki inganta tarbiyyar ’ya’yanki – Salamatu Ringim

Spread the love

“Sana’ar yajin daddawa sana’a ce mai matuƙar riba”

Daga UMAR AKILU MAJERI, a Dutse

Hajiya Salamatu Abdullahi wata mace ce da ta yi fice a kan harkar noman kaji da kiwon awaki ayankin ƙaramar Hukumar Ringim, baya ga wannan, ta kasance tana aiki a ma’aikatar ilimi ɓangaran kula da makarantun sakandire, fannin kula da nagartar ilimi.

Wakilinmu na Jihar Jigawa Umar Akilu Majeri, ya samu zantawa da Hajiya Salamatu akan hanyoyin da za su taimaka wajan inganta tarbiyyar yara ƙanana tare da matakan da za a ɗauka wajan magance matsalar da yake haddasa yawan mace-macen aure musamman a Arewacin Nijeriya.

Baya ga haka, Hajiya Salamatu ta shawarci mata da su rungumi harkar kiwo da noma, su guji zaman banza domin rashin abin yi a ɓangaran mata yana taimaka wa wajan samun mace-macen aure a ƙasar Hausa.

MANHAJA: Za mu so mu ji ko ke wacce ce.

HAJIYA SALAMATU: Daga farko dai sunana Salamatu Abdullahi Ringim na aikaciya a ma aikatar ilimi ɓangaran kula da makarantun sakandire, fannin kula da nagartar ilimi.

Haka zalika, ina yin sana’ar noma da kiwan kaji da awaki duk domin na taimaka wa yana da mijina domin wannan zamanin dole mata saibsun taimaka wa mazajensu ta ko wacce fuska saboda akwai ƙalubale a rayuwar da muke ciki a halin yanzu.

Kin ce ki na aikin gwamnati. Me ya sa kika shiga harkar kiwo da noma kuma kike kasuwancin yajin daddawa ?

Yajina da nake dakawa har saudiya ana kaishi, kuma ni idan na daka yajina har gida ake zuwa a saya, wani lokacin kuma odarsa ake yi online musamman idan nai magana na ɗora shi, kuma na tura wa abokaina da abokan kasuwanci za ka ga ana saya. 

Amma yanzu saboda tsadar citta da kanunfari da masoro ya sa bana iya sayan kayan yajin sun yi tsada, kuma sana’ar sana’a ce mai ribar gaske saɓanin yadda mutane suke tunani.

Kin ce ki na kiwo yaushe ne ki ka fara yin kiwon ?

Na fara yin kiwon kaji da kwaya biyar a cikin kwali a ɗakin dafa abinci, wato kitchen. Idan suka rayu na sayar da huɗu ko uku, mu yi farfesu da ɗaya, mu ci 

Yau an wayi gari Ina kiwata kaji 50 zuwa 70 a cikin gidana mijina ya ware min wani sashe na gidansa ina yin kiwan kajin da awaki.

Kuma Ina amfani da takin kashin kajin ina kai wa takin gona Ina amfani dabshi wajan yin noman shinkafa. 

Wato kenan, ki na noman shinkafa da dawa da gero ?

Gaskiya ne ina yin noman shinkafa da gero da dawa domin aƙalla a duk shekara Ina samun buhu goma sha uku na shinkafa, banda gero da dawa. Kuma noman yana taimakamin ta fuskar cigaban gidana.

Hajiya mene ne babban burinki a rayuwa ?

Burina shi ne, na ga na zama mace mai dogaro da kanta, wannan dalilin shi ne ya sa na rungumi harkar noma da kiwo domin akwai rufin asiri mai yawa a cikinta.

Domin wani zamani ne yanzu Allah ya kawomu mafiya yawancin mata su ne suke riƙe da gida ba maza ba saboda tsadar rayuwa da al’umma suka samu kansu a ciki, saidai fatan Allah ya yi mana da sauƙi.

Saboda haka akwai buƙatar mata su tashi tsaye wajan yin sana’ar kiwo da noma.

Yaushe ne ki ka fara kiwo da noma ?

Yau kimanin shekara goma sha takwas da fara kiwon kaji. Na fara yin kiwon kaji da guda biyar. Kuma na fara da ‘yan tsati biyar a lokacin idan na kiwata biyar ɗin sai na sayar da huɗu na bar man ɗaya mu yi farfesu.

A halin yanzu Ina kiwata kaji hamsin zuwa daba’in a ɗaki da mijina ya ware min nake kiwo agidansa. Kuma ni dana kajin nama nake kiwo domin sun fi kawo kuɗi su ba a cika yin hasara ba saboda basa ɗaukar lokaci mai tsawo.

Wacca shawara za ki ba wa mata ‘yan uwanki akan dogaro da kai?

Mata su zage damtse su tsaya suyi sana’a, su rufa wa kansu asiri da yaransu, domin sai suna da kuɗi ne za su samu cikakkiyar damar da za su inganta tarbiyar ‘ya’yansu. Saboda a yanzu muna wani zamani ne da Allah ya kawomu in ba kada kuɗi babu wanda ke ɗaukar maganarka, balantana ka yi magana a yadda da ita.

Hajiya, na gode.

Ni ma na gode.

By ukarofi