Yadda ake tuntuɓar JAMB don kai ƙorafi akan sakamakon jarrabawar UTME

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta fara sake duba tsarin jarrabawar gama-gari na shekarar 2025 da ta gabata sakamakon ƙorafe-ƙorafe da ɗalibai suka yi a faɗin ƙasar nan.

Hukumar jarrabawar ta JAMB, wacce ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME ta 2025 a ranar Juma’ar da ta gabata, ta amince da karɓar ƙorafin da ba a saba gani ba game samun ƙarancin maki a jarrabawar.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin da ta gabata, Hukumar JAMB ta ce ta na hanzarta bin diddigin matsalolinnda aka samu a jarrabawar.

Hakan ya ƙunshi matakai uku masu muhimmanci: rajista, jarrabawa, da sakin sakamako.

Hakan ya biyo bayan rahotannin rashin samun isasshen maki a cikin UTME da aka kammala kwanan nan.

Ga yadda ɗalibai za su kai ƙorafi a hukumance game da sakamakonsu:

1. A ziyarci shafin taimako na JAMB a https://www.jamb.gov.ng/support.

2. A danna “Create Support Ticket.”

3. Za a sa ka bayyana ko kai ɗalibin da ya rubuta JAMB ne ko kuma za ka kai ƙorafin ne a madadin wani.

4. Za ka cika fam ɗin sannan ka aika. A tabbatar an yi amfani da ingantaccen adireshin imel kuma a lura da lambar ID ɗin.

5. JAMB za ta sanar da kai ta hanyar imel da zarar ƙorafinka ya samu zuwa wurin ta.

6. Don bin diddigin martani, ziyarci https://support.jamb.gov.ng/candidate-support/my-tickets.ɗalibai ba sa buƙatar ziyartar Hedikwatar Hukumar ko ofisoshin jiha don gabatar da ƙorafi. Yakamata a shigar da duk ƙorafe-ƙorafe akan https://www.jamb.gov.ng/support.

By ukarofi