Har yanzu mata ba sa samun cikakken ‘yanci da mutuntawa – Hauwa Babaji 

Spread the love

“Zama mace dama ce ta zama gwarzuwa kuma jajirttacciya”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

MANHAJA: Waɗanne nasarori ki ka cimma kawo yanzu?

HAUWA: Alhamdulillah, duk da ƙananan shekaruna, akwai wasu manyan nasarori da Allah ya ba ni damar cimmawa a wannan tafiya. Na fara daga ƙanana ne, amma yanzu ni ce Kwamishiniya ta jiha, a ƙungiyar Nigerian Girl Guides Association a Gombe, inda nake jagorantar shirye-shirye da dama da suka shafi yara mata a fannoni daban-daban kamar wayar da kai kan jinin al’ada. 

Na kafa tawa ƙungiyar, wato Teens Care Foundation. Na yi aiki da manyan ƙungiyoyi da hukumomi, kuma na wakilci Jihar Gombe a wasu muhimman tarurruka da horo na ƙasa. 

Haka kuma, nasan cewa nasara ba a suna take ba, amma ana samun ta ne daga murmushi da kyakkyawan fata, da samun goyon baya da tallafi.

Wanne kira za ki yi ga matasa mata ýan’uwanki da ke fuskantar ƙalubalen a rayuwar su, saboda kasancewar su ýaýa mata?

Kirana ga ‘yan’uwana matasa mata shi ne su kula da kansu, su yarda da kansu kuma su san cewa su ma suna da daraja kamar kowa. Na san rayuwa na cike da ƙalubale kamar rashin goyon baya, talauci, auren dole, ko cin zarafi amma hakan bai kamata ya hana ki hangen gaba mai kyau ba.

Ina so su san cewa zama mace ba yana nufin ki zama mai rauni ba ne, dama ce ta zama gwarzuwa kuma jajirttacciya. Duk inda kika fito, komai ƙarancin damar da kike da ita, kina da ikon canza labarinki. Ki yi ƙoƙari ki nemi ilimi, ki nemi ilimin rayuwa (life skills), ki daina jin kunyar neman taimako idan kina buƙata.

Ki nesanta kanki da masu tauye miki ƙima ko wacce hanya ce da za ta hana ki kai burinki. Muryarki da burinki su ne abu mafi muhimmanci a duniyar nan. Duniya tana buƙatar muryar ki, ƙarfinki da hangen nesanki.

A ƙarshe, ina ƙarfafa su da su nemi haɗin kai da ƙungiyoyi kamar tamu domin samun horo, shawara da tallafi. Muna tare da su a kodayaushe.

Shin kin yarda mata ba sa samun cikakken ýanci da mutuntawa a wasu harkokin rayuwa a ƙasar nan?

E, gaskiya ne har yanzu mata ba sa samun cikakken ‘yanci da mutuntawa a fannoni da dama na rayuwa a ƙasar nan. Duk da cewa akwai dokoki da manufofi da ake faɗi-tashin cewa ana ƙoƙarin kawo daidaito, amma a aikace, mace tana fuskantar matsin lamba iri-iri daga al’umma, al’adu da ma tsarin rayuwa.

A wasu wurare, ana hana mace damar yin karatu saboda ita mace ce. Ana tilasta mata yin aure da wuri, ko kuma a hana ta yanke shawara kan lafiyarta, jikin ta ko ma rayuwar ta gaba ɗaya. A wasu ma’aikatu ko wuraren aiki, ba a ba mata dama irin ta maza ko dai saboda jinsinsu ko kuma saboda wani tunani na cewa mace ba za ta iya ba.

Muna da ƙalubale sosai a ɓangaren ganin mace a matsayin cikakkiyar ‘yar ƙasa da take da ‘yancin rayuwa kamar kowa. Amma ina da yaƙinin cewa da wayar da kai, da ilimi, da jajircewar irin namu ‘change is possible’. Yanzu haka mata da matasa mata suna tashi tsaye, suna magana, suna neman hakkokinsu cikin natsuwa da basira. Kuma wannan yana nuna cewa lokaci yana zuwa da mata za su samu cikakken girmamawa da ‘yanci da ya dace da su a kowane fanni na rayuwa.

Shin kina da ra’ayin zama ýar siyasa a nan gaba?

 E, ina da ra’ayin zama ‘yar siyasa a nan gaba, in sha Allah. Ba na zaɓi don mulki ko kujerar kaina ba, amma don in samu damar yin tasiri kai tsaye a cikin tsarin da ke yanke shawarar rayuwar mata da yara a ƙasar nan. 

Ayyukan da nake yi yanzu na nuna mini cewa sau da yawa matsalolin da muke fafutuka a kai na buƙatar tallafi daga matakin doka da gwamnati. Idan muka samu mata masu kishin al’umma da fahimtar matsalolin talakawa a cikin majalisa ko gwamnati, zai fi sauƙi a samar da dokoki da manufofi da za su amfanar da yara mata, matasa da ma al’umma gaba ɗaya.

Don haka, ina kallon siyasa a matsayin wata hanya da zan cigaba da hidima ga al’umma a babban mataki, tare da tabbatar da cewa muryar yara mata, matasa, da masu rauni tana da wakilci a wajen da ake yanke muhimman hukunci.

Wanne kira za ki yi ga mata ýan siyasa da ke matakai daban-daban, don su kawo wa yara mata ɗauki?

Kirana ga mata ‘yan siyasa da ke rike da madafun iko a matakai daban-daban shi ne su kasance wakilan gaskiya ga mata da yara mata. Ina roƙon su da su yi amfani da damar da Allah ya ba su wajen ƙirƙirar tsare-tsare da dokoki da za su bunƙasa rayuwar yara mata, musamman a fannoni kamar ilimi, lafiya, kariya daga cin zarafi da kuma bunkasa basirar su.

‘They should not forget where they started from’. Yawancinsu sun san irin ƙalubalen da mace ke fuskanta a al’umma saboda haka su zama jigo na kawo sauyi, ba kawai masu bin tsarin da ya ci gaba da tauye ‘yancin mace ba.

Ina ƙarfafa su da su tallafa wa ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki da yara mata a ƙasa, su buɗe damar samun scholarship, mentorship, da life skills trainings a makarantu da ƙauyuka.

A ƙarshe, su zama abin koyi ga sauran mata da yara mata, su nuna cewa mace na iya zama shugaba, mai tasiri, kuma mai ceto al’umma.

Kuna shiga ƙauyuka don gudanar da aikin wayar da kai ga mata. Wanne abu ne ya fi damunki kan halin da ake mata ke ciki a ƙauyuka?

E, muna shiga ƙauyuka akai-akai domin wayar da kai, musamman kan batutuwan da suka shafi yara mata kamar illimin su, jinin al’ada, cutar VVF, da kuma kan Gender Based violence. Abin da ya fi damuna sosai a ƙauyuka shi ne rashin ilimi da rashin dama ga mata, wanda ke hana su samun ci gaba kamar takwarorinsu na birni.

Yara mata da dama a ƙauyuka ba sa zuwa makaranta, ko kuma suna barin makaranta da wuri saboda auren dole, talauci ko kuma rashin wayewa daga iyaye. Wasu suna fama da jinin al’ada cikin wahala saboda babu pad, babu ilimi game da yadda za su kula da kansu kuma sukan ji kunya su nemi taimako. Haka kuma akwai waɗanda ke fama da VVF saboda auren wuri da rashin samun kulawa ta lafiya da ta jiki.

Abin da ke ƙara tada hankali shi ne yadda al’umma ke ganin waɗannan matsaloli a matsayin “na al’ada,” wato na yau da kullum, maimakon su ɗauke su da muhimmanci. Abin da yake damuna shi ne yadda aka mayar da irin waɗannan matsaloli a matsayin ba komai ba, ana ganin duk matsalolin da mace ke fuskanta tamkar dole ne ko ƙaddara ce.

Don haka, mu a matsayinmu na masu faɗakarwa muna ƙoƙari wajen canza wannan tunani ta hanyar ilimi, tattaunawa da horo domin mu tayar da hankali kan cewa mace ma tana da ‘yanci da damar rayuwa cikin kima da mutunci.

Mene ne burinki nan gaba a rayuwar ki?

Burina nan gaba a rayuwata shi ne in ci gaba da zama murya ga waɗanda ba su da damar yin magana musamman yara mata da matasa a karkara da birane.

 Ina son ganin Najeriya da duniya gaba ɗaya sun zama wuri da mace za ta iya rayuwa cikin kwanciyar hankali, da kuma samun damar cika burinta ba tare da takurawa ba.

Ina da burin faɗaɗa TeensCare Foundation domin ta riƙa kai wa ƙauyuka da dama a jihohi daban-daban na Najeriya, tare da samar da ƙrl inda yara mata za su rika samun ilimi, tallafi da horo kan zaman rayuwa da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Haka kuma, ina da burin cigaba da karatuna a matakin duniya a fannin lafiyar ƙwaƙwalwa, cigaban rayuwar mata, domin in samu ƙwarewa da ilimi da zan yi amfani da su wajen ciyar da al’umma gaba.

A ƙarshe, burina shi ne in ga wata rana wata yarinya daga ƙauye ko unguwar talakawa na cewa: “Na samu damar karatu, lafiya da cigaba saboda wani lokaci wata mace ta tsaya ta kare mu.”

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Karin maganar da take da matuƙar tasiri a rayuwata ita ce, “Idan ba mu faɗa ba, wa zai faɗa? Idan ba yanzu ba, sai yaushe?”

Wannan karin magana tana tunasar da ni cewa lokacin kawo sauyi yanzu ne, kuma kowane ɗan’adam na da rawar da zai taka. A matsayina na mace matashiya, tana ƙarfafa ni in farka kowacce rana da nufin yin abu mai amfani ko da ƙanana ne wanda zai amfanar da wasu, musamman yara mata.

By ukarofi