
Daga BELLO A. BABAJI
Masu-ruwa-da-tsaki na jam’iyya mai mulki (APC) sun koka game da tsamin alaƙa da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu duba da cewa babu alamar sulhu a tsakanin su.
Duk da cewa, babu wanda ya bayyana hakan ga al’umma a tsakanin mutanen biyu, muryoyi daga APC a matakin ƙasa da jihar sun tabbatar da samun rashin jituwa da ya raba tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnan.
Ziyarar da Tinubu ya kai wa jihar a kwanan nan ta ƙara buɗe al’amarin tun daga saukarsa a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed, inda aka fahimci akwai wani abu a tsakanin su a sakamakon tsallake gwamnan da gaisawa da mataimakinsa da Tinubu ya yi, lamarin da ake ganin da wata manufa ya yi hakan.
Hakan kuma an ji ƙishin-ƙishin ɗin cewa an umarci tawagar ƴan jarida na Shugaban Ƙasa da cewa kada su yaɗa ɗaukar filin jirgin musamman ma wajen da aka yi gaisuwar.
Sannan, an yi zargin cewa an umarci mataimaka da su cire duk wata ɗauka da za ta nuna cewa akwai tsamin dangantaka a tsakanin ɓangarorin biyu.
Wani babban jami’i kan tattaunawa ta cikin gidan gwamnati ya ce, an hana Gwamna Sanwo-Olu shiga sahun ƴan rakiyar Tinubu zuwa gidansa dake Ikoyi, wanda a ƙa’ida shi ne wanda ya dace ya jagoranci tawagar.
A madadin haka ne aka wakilta Hamzat ya raka shugaban ƙasar, lamarin da ya ƙara bayyana tsamin alaƙar, inji babban jami’in.
Bugu da ƙari, ba a ga gwamnan da mataimakansa ba a yayin ziyarce-ziyarce da wasu harkokin da Tinubu ya gabatar a jihar.
Har’ilayau, muryoyi daga Villa da APC’n Legas sun ce, tun da farko aka cire sunan gwamnan daga cikin waɗanda za su tarbi Shugaban ƙasar a yayin ziyarar tasa.
