“Ranar Hijabi ta Duniya ba ta Musulmai kaɗai ba ce”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Hajiya Fatima Suleiman Abdullahi ba ɓoyayyiya ba ce a garin Jos da wasu sassan Jihar Filato, inda ta shafe tsawon shekaru tana gudanar da ayyukan jinƙai da taimakawa al’umma, faɗakarwa da kuma sasanta tsakanin ma’aurata. Mace ce mai kishin ganin mata sun samu ilimi da sana’a, don su dogara da kansu. Duk da kasancewar ta babbar ma’aikaciyar gwamnati, amma aikinta bai hana ta shiga ƙauyuka da lunguna daban-daban ba, domin ta gana da raunanan mata da waɗanda rikice-rikice suka raba da mahallansu. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da ita a shafin Gimbiya, domin jin yadda rayuwarta ta amfani jama’a da burinta na ganin yara mata da ƙananan yara almajirai sun samu kyakkyawar rayuwa da ilimi mai inganci.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
HAJIYA FATIMA: Sunana Hajiya Fatima Suleiman Abdullahi. Ni malamar makaranta ce, ýar gwagwarmayar kare haƙƙoƙin mata da ƙananan yara. Ni ce shugabar ƙungiyar tallafawa cigaban rayuwar al’umma ta Integrated Community Development Initiatives of Nigeria, wacce ake yi wa laƙabi da ICIN. Kuma ni ce Mataimakiyar Magatakardar Kwalejin Nazarin Gandun Daji ta ƙasa da ke Jos, wato Federal College of Forestry.
Ko za ki ba mu tarihin rayuwarki?
Ni dai haifaffiyar garin Jos ce. Na yi makarantar firamare a Fatima Private School. Sai na shiga Baptist High School a matakin sakandire. Sannan na yi difloma akan aikin jarida a Jami’ar Jos, daga nan kuma na yi digirina na farko a aikin jarida da turanci. Na yi aikin koyarwa a wata makarantar sakandire da ake kira, College of Islamic Studies (CIS), a matsayin malamar Turanci. Bayan na shekara biyar ina koyarwa a CIS sai na koma koyarwa a wata makarantar sakandire ana ce mata Jabalun Noor, inda na yi shekara uku. A 2005 na je na yi digirina na biyu a ɓangaren nazarin aikin shari’a da diflomasiyya. A lokacin na fara tunanin aikin tallafawa al’umma, wannan shi ne sanadin kafa ƙungiyar ICIN a shekarar 2006. A wannan ƙungiya muna ba da tallafi a ɓangaren inganta rayuwar yara mata, inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, da kuma taimakawa marasa galihu, musamman bayan rikice-rikicen da aka fuskanta a Jos. Na fara aikin gwamnati a shekarar 2008 a Kwalejin Nazarin Raya Gandun Daji ta ƙasa, wato Federal College of Forestry Jos. A yanzu ni ce ke riƙe da kujerar Mataimakiyar Magatakardar Kwalejin.
Wacce gwagwarmaya ki ka sha game da batun neman ilimi?
Babu shakka na sha wahala sosai, a ɓangaren karatu, domin in ba don mahaifiyata ba da ban yi makaranta ba. Mamana ce ta ɗauke ni ta kai ni wurin wata ƙanwarta wacce ta mayar da ni makaranta a Fatima Private School, wacce makaranta ce ta ýan Mishan. A nan ne na fara samun damar yin karatuna na boko.
Yaya aka yi ki ka samu kanki a harkar ƙungiyoyin sa kai da kare ýancin al’umma?
Kishin taimakon al’umma, musamman mata, shi ne ya fara sa min sha’awar kafa ƙungiya. Ina son in ga ina taimaka wa mata, don in ga rayuwar su ta yi kyau, kuma suna iya dogaro da kansu, har ma su taimaki waɗansu, kamar gidajensu da ‘ya’yansu. Amma na koyi aikin tallafawa jama’a ne a wajen Kirista ýan mishan, da kuma wasu manyan mata da nake koyi da su. Kamar irinsu mamana, Hajiya Amina Abdullahi, Farfesa Jamila Nasir, Misis Aisha Esther Kwande, Farfesa Funmi Para Mallam, mni, da Misis Benedicter Daber.
Ke ce shugabar ƙungiyar nan mai zaman kanta ta ICIN, ko mene ne manufofin kafa ta, kuma waɗanne ayyuka ku ke yi?
E, babu shakka haka ne. Kamar yadda na yi bayani a baya ni ce na kafa ƙungiyar Integrated Community Development Initiative of Nigeria (ICIN), kuma muna gudanar da ayyukan jinƙai da suka shafi mata da ƙananan yara, nakasassu, da almajirai, da sauran mabuƙata. Ayyukan mu sun fi ƙarfi a ɓangaren ilimi, ba da shawarwari ga ma’aurata maza da mata, wato counselling, da kuma yin bita akan ‘yancin mata da haƙƙoƙinsu. Muna aiki da Jami’ar Jos a ɓangaren kyautata rayuwar yara almajirai, da koya musu ilimin boko da na addini a lokaci guda. Mun ci nasarar samun tallafin koya masu sana’o’in dogaro da kai, ba tare da sun yi bara ba, wanda suke koya a GSS Anguwar Rogo. Muna koyawa mata da marasa galihu sana’o’in dogaro da kai tare da haɗin gwiwar Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta NDE da Hukumar Tallafawa Masu ƙananan Sana’o’i ta Jihar Filato, wato PLASMEDA, inda ake koya masu tattalin ƙaramin jari, da yin adashe.
Muna kuma yin bita akan hanyoyin samar da zaman lafiya tare da tallafin manyan ƙungiyoyi masu zaman kansu irinsu Mercy Corps, British Council da Mission 21. Akwai kuma bita da muke yi akan tsafta da taimakawa mutane da gidajen sauro masu magani, don yaƙi da cutar maleriya. Muna yin gwaji da duba marasa lafiya kyauta, da ba da magani ga mata masu ciki da ƙananan yara. Shekara goma sha bakwai kenan muna ba da wannan tallafi da taimakon kamfanin NASCO Group.
Wanne tasiri ayyukan ku ke yi a rayuwar jama’ar da ku ke taimakawa?
ƙungiyar mu ta ICIN ta samar da wata cibiyar koyar da sana’o’i da muke kira da ICIN Learning Centre, a ƙarƙashin wannan cibiya, mun koyar da matasa maza da mata dabarun sarrafa na’urar kwamfiyuta da fasahohin zamani, girke-girke da gyaran fuska na mata, ɗinki, gyaran waya da sauran su. Mun horar da matasa fiye da 200 a cikin shekaru 17 da muka yi, wasu da dama a cikin su har sun buɗe nasu shaguna da wuraren kasuwancinsu. Bayan haka, muna da ɓangaren matasa na wannan ƙungiya, wanda yake da mambobi kimanin 70 maza da mata.
Yaya alaƙar ki take da sauran ƙungiyoyi da hukumomin gwamnati, wajen samar da cigaban al’umma?
ƙungiyar mu na alaƙa da hukumomin gwamnati, kamar irin su NDE, wato Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta ƙasa, inda muke tura mambobin mu da abokan hulɗarmu matasa, don koyon sana’o’in hannu irin su gyaran waya, aikin kwalliyar gini na zamani wato POP, aikin rini, da girke-girke. Sannan muna aiki da wasu hukumomin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu a ɓangaren inganta zaman lafiya, ƙarƙashin Hukumar Samar da Zaman Lafiya ta Jihar Filato, da Gamayyar ƙungiyoyin Tallafawa Ayyukan Samar da Lafiya, (PPPN), da masu ƙarfafa gwiwar mata wajen samar da ýanci da kare haƙƙoƙin juna, har da ma batun kiwon lafiya. Muna kuma haɗa gwiwa da wasu ƙungiyoyi irin su JDPC wajen samar da basussuka ga mata masu ƙananan sana’oi.
Jihar Filato, jiha ce mai haɗakar ƙabilu da addinai daban-daban, yaya ayyukan ku ke kawo zaman lafiya da fahimtar juna?
Kimanin shekaru 17 da kafuwar ƙungiyar mu, ayyukan mu sun yi tasiri sosai wajen sauya rayuwar mutane da dama. Muna da ma’aikata da muke aiki da su musulmi da waɗanda ba musulmi ba, har ma da marasa addini. Sannan ayyukan da muke yi ba su taƙaita ga al’ummomin da suke musulmi kaɗai ba, muna zuwa ƙauyuka inda mazauna wuraren ba musulmi ba ne. Muna ba su tallafi, musamman a aikin da muke yi ƙarƙashin kulawar Kamfanin NASCO.
Duk shekara ƙungiyar ku na shirya taron Ranar Hijabi ta Duniya, mene ne manufofin taron?
Kimanin shekaru 9 kenan muna shirya wannan taro duk shekara, da nufin faɗakar da iyaye da yara mata game da muhimmancin sanya sutura mai mutunci, kamar yadda addinin Musulunci ya koyar. Sannan a ilimantar da jama’a, musulmi da kirista, su fahimci cewa, hijabi ba sutura ce ta takura ko ƙuntatawa mata ba, sutura ce da ke ƙara wa mata ƙima da daraja. Sannan muna faɗakar da su yadda za su tsaftace kawunansu, da yadda mace mai hijabi ya kamata ta kasance, don bai dace mai hijabi ta aikata abin da bashi da kyau ba, irin su sace-sace da ɗaura bama-bamai don kisan ƙunar baƙin wake, a wuraren da ake rikice-rikice. Abin ban sha’awa ne jin cewa a lokacin da muke wannan taro muna gayyato har matan Kirista suna zuwa suna ganin abubuwan da muke yi, da suka shafi laccoci, faɗakarwa, gasar wacce ta fi iya sa hijabi da suturar mutunci, koyar da ɗaura hijabi, da waƙen baka.
Na lura da yadda ku ke gayyato waɗanda ba musulmi ba cikin bikin Ranar Hijabi ta Duniya da ku ke yi, wanne tasiri hakan ke haifarwa?
Babu shakka haka ne, muna gayyatar Kiristoci, wannan biki da muke yi na Ranar Hijabi ta Duniya, kuma muna gayyato ƙwararrun malamai da masana, da masu ruwa da tsaki, musulmi da waɗanda ba musulmi ba, domin su zo su saurari maganganu da koyarwa ta addini akan sanya Hijabi, har ma su koyi yadda ake naɗawa da saka shi. Muna kuma koyar musu cewa, sanya hijabi ba shi kaɗai ne abin buƙata ba, nuna kyakkyawan hali da biyayya ga koyarwar addini, su ne abin da ake buƙata ga Musulmi, har ma da wanda ba Musulmi ba. Ko su ma Kirista, musamman mabiya ɗariƙar Katolika, suna da irin wannan koyarwar, ta sanya sutura mai mutunci da za a rufe jiki. Ka ga kenan Ranar Hijabi ta Duniya ba ta Musulmi ba ce kaɗai.
Wanne irin jagoranci ku ke bai wa matasa a wannan ƙungiya?
Kamar yadda na faɗa a baya, muna da ɓangaren matasa, wanda muka kafa tun a shekarar 2020. Kuma ƙungiyar ta shafi samari ne da ýammata, da suke tsakanin shekara 18 zuwa 40. Mun kafa su ne saboda lura da muka yi akwai matsalar taɓarɓarewar tarbiyya a tsakanin matasa, da rashin ayyukan yi. Muna shirya musu bita akan illolin shaye-shaye, da shiga bangar siyasa, da kuma sanya su a wuraren koyon sana’o’i, don su iya riƙe kansu da kyautata rayuwarsu.
Mene ne saƙon ki ga al’umma game da taimaka wa juna da kama sana’o’i?
Shawarar da nake so na bai wa jama’a ita ce game da muhimmancin nuna tausayi da jinƙai ga mabuƙata, da kyautatawa waɗanda suke ƙarƙashin mutum, ko da masu aiki ne a gida ko ofis. Ba sai mutum ya daɗe yana maka bauta ko hidima ba, da zarar ya kai shekara biyu ko uku, a bashi dama ya koma karatu ko a sa shi a wajen koyon sana’a. Idan wata dama ta cigaba ta zo kada a yi wa mutum baƙin ciki, a taimaka masa ko ita, don su ƙara samun damar cimma burikansu na rayuwa. Hakan zai sa mutum ya samu damar riƙe kansa har ma ya taimakawa wasu na kusa da shi.
Kina daga cikin mata masu kishin cigaban ilimin ýaýa mata, yaya ki ke kallon sauyin da ake samu a nan Arewa?
Gaskiya ne. Ina da burin ganin rayuwar yara mata ta inganta. Ina so in ga yara mata sun samu damar shiga makaranta, sun yi ilimi, ko sun samu sana’a suna dogara da kansu. Ina so in ga mata sun samu ýanci da damarmaki na inganta rayuwarsu. Lallai yana da kyau a riƙa tallafawa rayuwar ýaýa mata, a kula da tarbiyyar su da cigaban rayuwarsu.
Wanne jan hankali za ki yi wa iyaye game da kula da ilimin ýaýansu da tarbiyyar su?
Ina so in ƙara jan hankalin iyaye mata, da ma dukkan iyaye, su mayar da hankali sosai ga tarbiyyar ýaýansu, saboda halin rayuwar da aka shiga. Lallai uwa tagari ta zama makarantar farko ta ýaýanta, ta sa ido sosai ga yadda rayuwar su take, da bambancin halayensu, don ta ba su tarbiyyar da ta dace. Duk da kasancewar tarbiyya ba ta uwa ba ce kaɗai, ta dukka iyaye ce. Amma mata na da nauyi fiye da maza saboda sun fi kasancewa kusa da yara fiye da iyaye maza. Mu sa ido sosai kan yaran mu da abokansu ko ƙawayensu da wuraren da suke zuwa, saboda makomar su ta gaba.
Wanne abin koyi ki ke so ki bar wa ýaýanki da sauran matasa da ke kallonki a matsayin abin koyi?
Abin koyi da nake so in bar wa matasa shi ne, kar su raina kansu. Kuma kar su raina sana’a kowacce iri ce. Kyakkyawar makoma tana farawa ne daga ƙuruciya mai kyau. Irin rayuwar da ka taso da ita tun kana ƙarami haka za ka yi bayan ka girma. Daga kan sanya sutura, iya magana, tsafta, riƙo da sana’a, neman ilimi, duk daga yarinta ake tashi da su. Matasa su ne manyan gobe, duk abin da ka shuka yau shi ne za ka girba gobe.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ki?
In ka ƙi ji ba ka ƙi gani ba.
Na gode.
Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.
