Daga UMAR GARBA a Katsina
Shugaban masu riƙe da sarautun gargajiya na jam’iyyar APC, Dakta Talba Abubakar ya yi kira ga Sarkin Daura da ya gaggauta tuɓe wa fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Rarara rawaninsa na sarkin waƙar ƙasar Hausa, bisa zargin yin waƙoƙin cin mutuncin tsohon ministan sadarwa, Malam Isa Ali Pantami.
Talba Abubakar ya buƙaci a tuɓe rawanin mawaƙin a cikin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce bai kamata ya ci gaba da kasancewa da muƙamin ba sakamakon waƙoƙin da ake zargin ya yi kan Farfesa Isa Ali Pantami ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe.
