
Shugabar Ƙungiyar Masu Buƙata ta Musamman ta Ƙaramar Hukumar Bichi, ta kai ziyara a majalisar ƙaramar hukumar domin neman ƙarfafa gwiwar bunƙasa sana’o’insu.
A sanarwar da Jami’ar Yaɗa labarai ta yankin, Jamila Abdullhi Rijiyar Lemo ta fitar, Daraktan Mulki, Alhaji Abba Muhammad Ɗiso, ya karɓi baƙuncinta a ofishinsa da ke sakatariyar yankin a madadin Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya yi alƙawarin tallafa wa Shugabar ƙungiyar ta hanyar bunƙasa tattalin arziƙin yankin baki ɗaya.
“In sha Allahu zan shigar da wannan koke na wannan yarinya ga Shugaban ƙaramar hukuma domin a taimaka mata, kuma mu ƙarfafa mata gwiwa mu haɗa ta da (Women Development Officer) ta wannan ƙaramar hukuma domin a haɗa ta da wasu matan; kodai masu buƙata ta musamman irinta ko kuma sauran mutanen gari gaba ɗaya domin ta koya musu sana’a,” inji Abba Muhammad Ɗiso.
Shugaban Sashen Walwala da jin Daɗin Jama’a na yankin, Malam Ibrahim Isyaku Shanono, duba da irin wannan hoɓɓasa da ta yi na taimakon kai da kai ta hanyar tsayawa da ƙafafunta duk da ta kasance mai buƙata ta musamman, ya nuna gamsuwa ɗari bisa ɗari na irin yadda ƙaramar hukumar ta rabauta da irinsu a cikinta, a yayin da ya bayyana cewa Ciyaman ɗin ƙungiyar tasu ma Alhaji Nura, bakanike ne da jama’a, musamman matasa ke koyon sana’ar kanikanci a wajensa a ƙaramar hukumar.
“Dama aikin hukuma ne ta ɗora su a kan layin samar wa kansu abin yi, a maimakon su dinga barace-barace. Alhamdu lillahi! A cikinsu ga shi wasu sun samu horon sana’o’i masu kyau sun gina kansu a kashin-kansu ta yadda za su iya koya wasu ma; yanzu ita wannan a ko’ina har cikin kasuwannin garin Kano ana sayan kayayyakinta katon-katon, wannan abin a ƙarfafe su ne hukuma ta shigo ciki wajen ba su
jari!” Ibrahim Isyaku Shanono.
A ɓangaren jami’ar kuka da ci-gaban mata ta sashen, Hajiya Aisha Abubakar, ta jinjina irin namijin ƙoƙarin shugabar ƙungiyar matuƙa gaya, inda ta ce, da yardar Allah za su samu taimakon da yakamata a ƙarƙashin ofishinta domin su ci gaba da dogaro da kansu yadda yakamata.
Ta kuma ce, ba su kaɗai ba, hatta sauran mutane waɗanda suka bambanta da su za su ci gajiyar wannan basira ta su a ɗaukacin yankin da ma jiha da ƙasa baki ɗaya ta hanyar faɗaɗa sana’o’insu, bisa yadda za su tsaya tsayin daka wajen tura su dukkan wasu santoci na ƙaramar hukumar domin koya wa ɗalibai yara ‘yan makaranta da matan aure ire-iren waɗannan sana’o’i nasu.
Tun da fari, a jawabin Shugabar Ƙungiyar masu Buƙatar ta Musamman, Hansa’u Ɗahiru, ta bayyana abubuwan da take sarrafawa na sana’ar sun haɗa da; sabulun wanka da wanke kai, man shafawa, man kitso, turare na ɗaki da na jiki, ta dai ce a ƙalla tana yin abubuwa na sana’a kusan kala 30 daban-daban.
Kazalika, ta ce ta fara harkokin sana’a ne tun tana ‘yar shekara 10, inda ta samu agajin farko na jari daga iyayenta, don haka a yanzu tana buƙatar tallafin gwamnati domin cika burinta na koya wa sauran al’umma irin wannan sana’a da take amfanarta a matakin ƙaramar hukuma da ma jiha gaba ɗaya.
“Idan na shiga kasuwa duk wanda ya gan ni ko bai yi niyyar siyan kayana ba yana tausaya min ya ce, ‘yadda kike haka, amma kina ɗauko kaya kasuwa ki sayar? Babu ruwanki da barace-barace!’ Nakan ce, to ai bara wulaƙanta kai da tozarta kai ne! Don haka, ina kira ga gwamnati don Allah a taimaka mana da jarin da zamu koya wa masu buƙata ta musamman waɗannan sana’o’i, ba ma iya su kaɗai ba da sauran mata da suke gida ba su da sana’a, za mu iya koya musu a kodayaushe.’ Hansa’u Ɗahiru.




