
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci a yi cikakken bincike kan mutuwar masu haƙar ma’adinai a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Neja bayan wani atisaye a yankin Mohammed Inuwa Wishishi Estate da ke Minna.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta lamunci mutuwar mutane da dama ba a saboda sakacin hukuma da gazawar bayar da kariya ga rayukan da aka ba ta amanar kula da su.
Shugaba Tinubu ya ce rayuwar kowane ɗan ƙasa tana da muhimmancin da bai dace ba a ce an rasa ta a hannun gwamnati saboda sakaci, cin zarafi ko nuna rashin tausayi, lamarin da ya zama wajibi a yi bincike a kai tare da tabbatar da adalci.
Ya bayyana cewa, kasancewar waɗannan mutane ana zargin su da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa doka ba ba hujja ba ce tauye musu ‘yancin rayuwa, mutunci da mu’amalantar su ta hali rashin tausayawa a ƙarƙashin hukumar gwamnati, yana mai cewa wajibi ne a hukunta dukkan wani jami’i da aka samu da hannu a ciki.
Akan haka ne shugaban ƙasar ya umarci hukumomin tsaro masu alhakin kula da lamarin da su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da gaskiya da adalci akan dalilan kamen, halin da aka ajiye su a lokacin da aka kama su, adadin waɗanda aka kama, kulawar da aka ba su da kuma abin d ya sabbaba mutuwarsu.
Kazalika, Shugaba Tinubu ya miƙa saƙonsa na ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, yana mai addu’ar samun rahama ga ruhinsu. Har ila yau, ya roƙi iyalan da ‘yan yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankali, tare da tabbatar musu da cewa an gano haƙiƙanin gaskiyar al’amarin tare da ɗaukar matakan doka a kai.
