Wani babban jami’in EFCC na fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani babban jami’in gudanarwa mai muƙamin Assistant Commander (ACE) a Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati (EFCC) ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa, amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba, daƙile shari’a da kuma mallakar dukiya mai yawa wadda ake zargin ba ta dace da abin da yake samu a matsayin albashi ba.

Zarge-zargen na ƙunshe ne cikin wata takarda mai shafuka shida da ƙungiyar Network for Justice Association of Nigeria (NJAN) ta miƙa wa Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ranar 9 ga Yuli, 2026, wadda Blueprint Manhaja ta samu kwafinta.

Wannan ƙorafi ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara mayar da hankali kan zarge-zargen rashin da’a a cikin EFCC, ciki har da wani bincike daban da ya shafi wani shugaban sashe kan zargin karɓar cin hancin dala 400,000.

Olukoyede ya sha nanata cewa tsaftace hukumar daga cin hanci da rashawa na cikin gida na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sahihancin yaƙin da EFCC ke yi da rashawa. Hukumar ta kuma ɗauki matakin ladabtarwa da korar wasu ma’aikata da aka samu da laifin damfara, rashin da’a da sauran take dokokin aiki.

Sai dai sabon ƙorafin ya ƙunshi manyan zarge-zarge kan wani babban jami’i da ake cewa yana da kusanci da shugabancin hukumar, wanda ake cewa albashinsa na wata-wata yana tsakanin N800,000 zuwa N900,000.

Shugaban NJAN, Adedeji Sunday Ajala, ne ya sanya hannu kan ƙorafin, wanda aka kuma aika wa Antoni-Janar na Tarayya, Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta ƙasa (DSS), Shugaban Hukumar ICPC da kuma Shugaban Code of Conduct Bureau (CCB).

NJAN ta lissafa zarge-zarge guda 21 da ake yi wa jami’in, waɗanda suka haɗa da amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba, karɓar kuɗi ta hanyar matsin lamba, tsoma baki cikin bincike, samun damar bayanan sirrin harkokin kuɗi ba tare da izini ba, da kuma mallakar dukiya da ake ganin ba ta yi daidai da halastaccen abin da yake samu ba.

Blueprint Manhaja ta ce ba ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge da kanta ba, sannan takardar ƙorafin ba ta kawo wata hujjar cewa an taɓa yanke wa jami’in hukunci ko kuma wata hukuma ta same shi da laifin aikata waɗannan abubuwa ba.

A cewar takardar, wasu mutanen da suka bayar da bayanan da aka yi amfani da su wajen ƙorafin sun nemi a ɓoye sunayensu saboda tsoron fuskantar matsin lamba ko ɗaukar fansa a cikin hukumar. Sai dai NJAN ta ce zarge-zargen sun samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin “bayanai masu maimaituwa da abubuwan da ake iya lura da su”, waɗanda za a iya tabbatar da su ta hanyar bincike mai zaman kansa.

ɗaya daga cikin manyan zarge-zargen shi ne cewa jami’in yana gabatar da kansa a matsayin “lifeline” na Shugaban EFCC, inda ake zargin yana amfani da iƙirarin kusancinsa da shugabancin hukumar wajen yin tasiri a harkokin cikin gida.

Masu ƙorafin sun ce jami’in kan tsallake wasu matakan gudanar da aiki ta hanyar samun amincewa kai tsaye daga Shugaban EFCC, maimakon bin hanyoyin da suka dace ta hannun shugabannin da ke kula da ayyukan, ciki har da Head da Director of Operations.

Sun kuma zarge shi da cewa a wasu ƙorafe-ƙorafe yana neman kashi 10 cikin 100 na kuɗin da ake magana a kai kafin a fara bincike, sannan a wasu lokuta yana samun amincewa da ƙorafe-ƙorafe ba tare da an bi tsarin tantancewa na yau da kullum na hukumar ba.

Wani zargi kuma ya shafi samun bayanan sirrin asusun bankunan mutane. NJAN ta yi zargin cewa jami’in yana aiki tare da wasu abokan hulɗa a bangaren harkokin kuɗi domin samun bayanan mutane da kamfanoni, waɗanda daga bisani ake amfani da su wajen karɓar kuɗi ta hanyar matsin lamba maimakon amfani da su wajen ingantaccen bincike da gurfanar da masu laifi.

ƙungiyar ta kuma zargi jami’in da gudanar da wasu tarurruka da ake ɓoye tare da wasu fitattun waɗanda ake zargi da laifuka, a ciki da wajen harabar EFCC, inda ake zargin ana tattauna yarjejeniyoyin warware matsaloli ba bisa ƙa’ida ba da kuma abin da ake kira “soft landing”.

Takardar ta ce an yi zargin cewa an ɗauki wasu daga cikin waɗannan ganawa a faifan bidiyo, kuma ana iya gudanar da bincike a kansu. Daga cikin zarge-zargen da suka fi tsanani akwai cewa jami’in ya karɓi makudan kuɗaɗe na Naira da kuma kuɗaɗen ƙasashen waje ta hannun wasu wakilai, domin bai wa waɗanda ake zargi da laifuka sauƙi.

NJAN ta kuma yi zargin cewa an taɓa gaya wa wasu mutane ƙarya cewa an saka sunayensu cikin jerin mutanen da hukumomin tsaro ke sa ido a kansu, da nufin karɓar kuɗi daga gare su. Ta kuma zargi jami’in da haɗa kai da wasu ’yan siyasa wajen amfani da matakan EFCC kan abokan hamayyarsu, ciki har da zargin tsoma baki cikin bayar da belin gudanarwa domin samun kuɗi.

Masu ƙorafin sun kuma nemi a binciki dukiyar jami’in, wadda suka ce ta yi nisa fiye da abin da halastaccen abin da yake samu zai iya samarwa. Sun ambaci motocin alfarma, gidajen bene da ake zargin an mallaka ta hanyar wani kamfanin gine-gine, da kuma wasu kadarori a Dubai da ake cewa an saya ta hannun wani kamfanin sayar da gidaje.

NJAN ta yi zargin cewa an yi amfani da sama da dala miliyan ɗaya a matsayin kuɗin tsabar kuɗi wajen wasu sayayyar kadarorin ƙasashen waje, ciki har da wata ma’amala da ake zargin ta kai dala 300,000 a watan Yuni 2026. Sai dai PRNigeria ta ce ba ta iya tabbatar da waɗannan zarge-zargen da kanta ba.

Takardar ta kuma yi tambaya kan yawan tafiye-tafiyen jami’in zuwa Amurka a ajin kasuwanci, tare da zargin cewa yana da wata kadara a can. NJAN ta nemi a binciki bayanan shige da fice da kuma harkokin kuɗinsa.

ƙungiyar ta kuma nemi a binciki wani kamfanin kiwon kaji da ake alakanta shi da jami’in, bisa zargin cewa wataƙila ana amfani da kasuwancin a matsayin wata hanya ta ɓoye harkar safarar kuɗi ta hanyar kasuwanci, kodayake takardar ba ta kawo wani hukunci ko binciken hukuma da ya tabbatar da hakan ba.

NJAN ta kuma yi zargin cewa jami’in yana da alaƙa da wasu manyan ’yan siyasa da ’yan kasuwa masu tasiri, waɗanda muradunsu za su iya yin karo da ayyukan da yake gudanarwa a matsayin jami’in EFCC.

A wani misali, takardar ta yi zargin cewa wani fitaccen ɗan kasuwa daga Kudu maso Gabashin Nijeriya ya tuntubi jami’in domin ya yi tasiri kan wani shari’a da ke gaban hukumar. An kuma yi zargin cewa jami’in ya ziyarci gidan ɗan kasuwar da ke Abuja ranar 1 ga Yuni, 2026, inda ake zargin an ba shi wani adadin kuɗin dalar Amurka domin a dakile batun.

Takardar ta kuma yi zargin cewa jami’in yana da hulɗa da wasu ’yan siyasa a Arewacin Nijeriya, ciki har da wasu mutanen da ake alakanta su da shari’o’in da ke ƙarƙashin kulawarsa.

NJAN ta yi gargadin cewa idan aka tabbatar da waɗannan zarge-zargen, irin wannan hulɗa na iya jefa sahihancin EFCC cikin haɗari, rage amincewar jama’a ga yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da raunana gwiwar jami’an hukumar da ke gudanar da ayyukansu bisa ƙa’ida.

Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci Olukoyede ya ƙaddamar da cikakken bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen, tare da tabbatar da cewa an kare duk wasu shaidu da za su iya taimakawa wajen binciken, sannan a ɗauki matakin da ya dace idan aka tabbatar da aikata ba daidai ba.

Takardar ta ce: “Cikakken bincike da ɗaukar mataki mai ƙarfi zai ƙara tabbatar da amincewar jama’a ga ƙudurin hukumar na yin riƙon amana, tare da aika saƙo karara cewa babu wani jami’i, komai matsayinsa ko irin tasirin da yake da shi, da ya fi ƙarfin doka.”

Da Blueprint Manhaja ta tuntuɓi mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce hukumar na da tsauraran matakan rashin amincewa da cin hanci da rashawa a cikin gida.

Oyewale ya ce an kori sama da ma’aikatan hukumar 40 a baya-bayan nan, bayan an gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa a kansu.

Ya ƙara da cewa binciken ladabtarwa na cikin gida na ci gaba da gudana, sai dai ya ce a lokacin da aka tuntuɓe shi bai samu labarin wannan sabon ƙorafin da aka shigar kan jami’in ba.

By ukarofi

Leave a Reply