2027: Kungiyar mata Musulmi daga Arewacin Nijeriya ta goyi bayan Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ƙalla malaman addinin Musulunci mata 500 da suka fito daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Matan, ƙarƙashin ƙungiyar Muslim Intellectuals Forum, sun bayyana matsayinsu ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi.

Sun ce sun yanke wannan matsaya ne bisa la’akari da abubuwan da suka ce gwamnatin Tinubu ta cimma a fannonin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.

A cikin wata sanarwa da Aisha Iliyasu Tukur daga Jihar Jigawa ta karanta bayan taron, matan sun ce za su goyi bayan Tinubu domin ya samu damar ci gaba da shirye-shiryensa, kammala ayyukan da ake yi da kuma zurfafa sauye-sauyen da ake yi domin inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

Sun kuma yaba da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFund), inda suka ce shirin ya taimaka wajen ƙara damar samun ilimin manyan makarantu tare da rage wa ɗalibai da iyalansu nauyin kuɗin karatu.

Matan sun kuma yaba da matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka wajen inganta tsaro, ciki har da ƙarfafa rundunonin soji, samar da kayan aiki da ɗaukar ƙarin jami’an tsaro.

Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara mayar da hankali kan tsaro, ilimi, samar da ayyukan yi, ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce goyon bayan matan ba ya samo asali ne daga son kai ko ƙabilanci, sai dai saboda abin da suka ce gwamnatin Tinubu ta gudanar.

Ya ce matan sun fito daga sassa daban-daban na Arewa ne domin bayyana goyon bayansu ga shugaban ƙasa bisa manufofi da ayyukan gwamnatinsa.

Shi ma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu, yana mai cewa gwamnonin Arewa da al’ummar yankin za su tsaya tare da shugaban ƙasa.

Yahaya ya yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da su kasance masu haɗin kai tare da guje wa duk wani yunƙuri na raba kan jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply