Gwamnatin Sokoto ta rufe masallacin Lukuwa, ta kafa kwamitin bincike kan rikicin addini

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Musa Lukuwa da ke Mabera, cikin birnin Sokoto, biyo bayan harin da aka kai wa malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa gwamnatin ta kuma ayyana masallacin a matsayin wurin da ake gudanar da binciken laifi, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin rikicin.

Jaridar ta tuna cewa wani matashi daga cikin masu ibada ya kai wa Sheikh Lukuwa hari da wuka jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar Juma’a. Rahotanni sun ce matashin ya ji wa malamin rauni a wuya da hannu, kafin daga bisani a garzaya da shi Asibitin Kwararru na Sokoto domin kula da lafiyarsa.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da cewa malamin ya tsira daga harin, kuma daga baya aka sallame shi daga asibiti bayan an ba shi magani.

Rahotanni sun ce lamarin ya haifar da tashin hankali a wasu sassan birnin Sokoto, inda aka samu zanga-zanga tare da rufe wasu wuraren kasuwanci na ɗan lokaci.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan an gudanar da jerin zanga-zanga biyo bayan ci gaba da tsare wani malamin addini, Dahiru Mai Barewa, wanda ake zargi da yin barazana ga Sheikh Musa Lukuwa da wani malami, Malam Murtala Bello Assada.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnatin Jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ce ba za ta bari wasu mutane su yi amfani da addini wajen haifar da rikici ko rashin mutunta Annabi Muhammad (SAW), iyalansa da sahabbansa ba.

Gwamnatin ta kuma kafa kwamitin malaman addinin Musulunci (ulama) domin binciken abubuwan da suka haifar da rikicin addini na baya-bayan nan a birnin Sokoto, tare da ba gwamnati shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya.

Ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su guji kalaman tsokana ko na tayar da hankali, tana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen kare zaman lafiya da haɗin kan al’ummar jihar.

Gwamnatin ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro da kwamitin malaman addinin ke gudanar da bincike.

By ukarofi

Leave a Reply