
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma ciki a makonnin baya.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da gwamnatin jihar Kaduna ta yi da aiwatar da cikakken yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da ASUU ga jami’ar.
A wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar, Abubakar Abdullahi da Sakatarenta Silas Bakut suka aike wa ‘yan jarida, ASUU ta ce an ɗauki wannan mataki ne yayin zaman da ta gudanar a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026, wanda ya fara aiki da misalin ƙarfe 12:01 na safiyar Juma’a, 18 ga Satumba.
Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya amince da aiwatar da yarjejeniyar ta FGN-ASUU ta 2025, wanda za a fara gani daga albashin Oktoban 2026. Sannan, majalisar jagorancin jami’ar da hukumar gudanarwarta sun amince da biyan bashin albashin wata tara, wanda zai warware na daga Junairu zuwa Satumba.
ASUU ta kuma yaba wa gwamnatin jihar Kaduna, tawagar wakilan tattaunawarta da hukumar gudanarwar jami’ar bisa warware rikicin ta hanyoyi masu tsari, tana mai godiya kan yadda aka kawo ƙarshen matsalar ba tare da wulaƙanci ba ko wata barazana.
