Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta ƙaddamar da wani kwamiti da ya ƙunshi masu ruwa da tsaki da ƙwararru a fannin ilimi, domin samar da tsarin shigar da koyarwar kwarewar rayuwa da tunani mai zurfi cikin Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta bai ɗaya, wato UTME.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Magatakardar JAMB, Farfesa Segun Aina, ne ya ƙaddamar da kwamitin ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matakin na da nufin tabbatar da cewa UTME ta dace da sauye-sauyen da ake samu da kuma buƙatun ilimin manyan makarantu a wannan zamani.
Aina ya ce ainihin aikin UTME shi ne tantance matsayi da cancantar ’yan takarar da suka riga suka samu takardar shaidar O’Leɓel, don haka bai kamata jarabawar ta sake maimaita irin tantancewar da Majalisar Jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da Majalisar Jarabawar Nijeriya (NECO) suka riga suka gudanar ba.
A cewarsa, an riga an tantance ’yan takara kan ilimin darussan da suka koya tun matakin O’Leɓel.
“Saboda haka aikinmu shi ne tantance matsayi. Ba lallai ba ne mu gwada ƙwarewar ɗan takara kai tsaye kan ilimin darasin da ya karanta.
“Don haka muna ganin idan UTME za ta kasance kawai ta gwada ilimin darussa, hakan zai zama wani nau’in maimaita aiki,” inji Aina.
Ya ce JAMB na son tantance ƙwarewar da ’yan takara za su iya amfani da ita wajen fuskantar al’amuran rayuwa, tare da duba ko tsarin UTME na yanzu har yanzu yana da tasiri wajen gano ’yan takarar da za su iya yin nasara a manyan makarantu.
Ya yi tambaya kan ko hanyoyin da JAMB ke amfani da su wajen gano da kuma hasashen waɗanda za su yi nasara a jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi har yanzu suna da inganci.
Aina ya lura cewa UTME ta ci gaba da kasancewa cikin tsarin da bai samu manyan sauye-sauye ba tsawon sama da shekaru 30, yana mai cewa ya zama dole a duba tsarin jarabawar domin ya dace da sauye-sauyen da ake samu a fannin ilimi.
“Babban ɗaki a cikin gida shi ne ɗakin da ake iya ingantawa. Don haka muna son kwamitin ya taimaka mana wajen duba wannan batu,” inji shi.
Magatakardar ya ce an tattaro wakilai daga sassa daban-daban na fannin ilimi ne cikin kwamitin saboda JAMB ba za ta iya yanke shawarar hanyar da ta fi dacewa da wannan gyara ita kaɗai ba.
“Ba za mu iya zama alƙalai a cikin lamarin da ya shafe mu da kanmu ba.
“Mun tattaro masu ruwa da tsaki da ƙwararru domin su binciki batun, su ba mu jagoranci, tare da tabbatar da cewa duk shawarar da aka ɗauka za ta kasance abin karɓa ga duk waɗanda za ta shafa,” inji Aina.
Ya bayyana aikin kwamitin a matsayin nauyin da ya shafi ƙasa baki ɗaya, inda ya ce an ba kwamitin wa’adin farko na makonni huɗu domin nazarin batun daga mahangar tsari da tunani.
Shi ma da yake jawabi, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, wanda Mataimakinsa na Fasaha, Oni Adedeji, ya wakilta, ya ce shirin ya yi daidai da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin tsarin tantance ɗalibai a fannin ilimi.
Alausa ya buƙaci kwamitin da ya samar da tsarin tantancewa mai inganci, adalci da gaskiya, wanda zai auna ƙwarewar ’yan takara wajen nazarin al’amura, tunani mai ma’ana da fahimtar magana, ba wai iya haddace abin da suka koya a darussa kawai ba.
Ya ce kwamitin zai kuma duba yadda za a shigar da abubuwan da suka shafi kwarewar rayuwa da tunani mai zurfi, ko dai a matsayin wata jarabawa ta daban da za a daidaita tsarinta, ko kuma a saka su cikin darussan da ake yi a UTME a halin yanzu.
“Gyaran na da nufin samar da tsarin tantancewa wanda ba zai gwada abin da matasan Nijeriya suka sani kawai ba, har ma da yadda suke iya tunani, nazari da warware matsaloli yadda ya kamata.
“Ina da yakinin cewa samun wannan daidai zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda Nijeriya za ta tantance shirye-shiryen matasa na shiga manyan makarantu a yanzu da kuma shekaru masu zuwa,” inji shi.
Ministan ya tabbatar wa kwamitin cewa ma’aikatar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da kuma ba shi cikakken goyon baya yayin gudanar da aikin.
Da yake mayar da martani, Shugaban kwamitin, Farfesa Boniface Nworgu na Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka, ya ce ya kamata a auna ingancin UTME bisa yadda take iya gano ’yan takarar da ke da kyakkyawar damar samun nasara a karatun manyan makarantu.
Nworgu ya bayyana cewa JAMB tana gudanar da jarabawar zaɓe ne, ba jarabawar bayar da takardar shaidar kammala karatu ba, don haka yana da muhimmanci jarabawar ta iya hasashen damar ɗan takara na samun nasara a fannin karatu.
“Abin da ake sa ran JAMB za ta yi, kuma abin da take yi, shi ne duba matakan da za su taimaka mana wajen zaɓar ’yan takarar da ke da mafi kyawun damar samun nasara a ayyukan ilimi a matakin manyan makarantu,” inji shi.
Ya ce ya kamata a riƙa duba ingancin UTME lokaci zuwa lokaci saboda tsarin karatun manyan makarantu da kuma ƙwarewar da ake buƙata sun sauya tsawon shekaru.
A cewarsa, sauyin tsarin karatun jami’o’i daga Benchmark Minimum Academic Standards (BMAS) zuwa Core Curriculum and Minimum Academic Standards (CCMAS) ya ƙara jaddada muhimmancin ƙwarewa da tunani mai zurfi.
“Yanzu an fi mayar da hankali kan ƙwarewa da kuma tunani mai zurfi. Saboda haka, abin da JAMB ke ƙoƙarin yi ana iya fahimtarsa ta wannan fuska,” inji Nworgu.
Sai dai ya ce kwamitin zai kasance a buɗe wajen duba wasu matakai da za su iya inganta ikon UTME na gano ’yan takarar da ke da damar samun nasara a manyan makarantu.
“Idan a yayin tattaunawarmu muka gano cewa akwai wasu matakai da za su iya inganta ingancin hasashen UTME, tabbas za mu gabatar da shawarwarin da suka dace,” inji shi.
Nworgu ya jaddada muhimmancin amfani da hujjoji da bayanai wajen tantance ko sauye-sauyen da za a shigar cikin UTME suna cimma manufofin da aka sanya musu.
“Ba za mu yi wannan kuskuren a wannan karon ba,” inji shi.
Ya bayyana cewa dole ne a samu ingantaccen tushe da za a iya amfani da shi wajen auna tasirin duk wani sauyi da aka shigar cikin tsarin jarabawar.
Nworgu ya tabbatar wa JAMB cewa kwamitin a shirye yake ya gudanar da aikin tare da gabatar da shawarwarinsa cikin wa’adin da aka tsara.
Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga jami’o’i, hukumomin shirya jarabawa, hukumomin kula da sana’o’i, ƙungiyoyin ɗalibai, makarantun sakandare da ƙungiyoyin ci gaba.
