Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su, tare da kashe ’yan ta’adda biyu a wasu ayyukan samame da suka gudanar a jihohin Katsina da Kebbi.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, dakarun sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa ’yan ta’adda a wasu ayyuka daban-daban da suka gudanar a jihohin biyu.
Jami’in Yaɗa Labarai na Operation FANSAN YAMMA, rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 16 ga Satumba, 2026.
A cewar sanarwar, ayyukan da aka gudanar a ranakun 14 da 15 ga Satumba, 2026, sun kuma kai ga kwato harsasai, babur, kayan sojoji na kama-karya da wasu kayayyaki.
A jihar Katsina, dakarun Sector 2 sun ceto mutane 10, ciki har da maza uku da mata bakwai, bayan sun samu rahoton sace mutane daga garuruwan Unguwan Daudu da Unguwan Chibauna da ke ƙaramar hukumar Funtua ranar 14 ga Satumba.
Dakarun sun yi gaggawar bin sawun ’yan ta’addan tare da fafatawa da su a musayar wuta, lamarin da ya kai ga ceto mutanen, ciki har da wani jariri.
An kai mutanen da aka ceto hannun jami’an soji domin ɗaukar matakan da suka dace.
A wannan rana, dakarun da ke jihar Kebbi sun mayar da martani ga kiran gaggawa bayan da aka yi garkuwa da wasu fararen hula daga ƙauyen Fafala da ke ƙaramar hukumar Kangiwa.
Sanarwar ta ce, bisa ingantaccen bayanan sirri, dakarun sun gudanar da sintirin yaƙi zuwa Fafala da Dandikwa, inda suka yi arangama da ’yan ta’addan a wata musayar wuta mai tsanani, lamarin da ya tilasta musu ja da baya.
Bayan haka, ci gaba da aikin da dakarun suka yi a yankin ya kai ga ceto mutane 21, waɗanda daga bisani aka haɗa su da iyalansu.
A ranar 15 ga Satumba kuwa, dakarun da ke jihar Katsina sun dakile wani shirin da ake zargin ’yan ta’adda na yi na kai hari kan wasu al’ummomi a ƙananan hukumomin Matazu da Kankara.
Dakarun, bayan samun ingantaccen bayanan sirri, sun nufi maboyar ’yan ta’addan tare da tunkarar su da ƙarfin wuta, inda suka kashe ’yan ta’adda biyu, ciki har da Abbah Alhassan, wanda rundunar sojin ta bayyana a matsayin sanannen jagoran ’yan ta’adda.
Rahoton ya ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun tsere zuwa cikin daji da ke kewaye da yankin.
Daga cikin abubuwan da aka kwato a wurin akwai harsasai 10, babur guda ɗaya, adda guda ɗaya, kayan sojoji na kama-karya da kuma tabar wiwi, da wasu kayayyaki.
A wani samame na daban da aka gudanar a wannan rana, dakarun sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa ’yan ta’adda a yankin Yantumaki da kewaye, da ke ƙaramar hukumar Dan Musa a jihar Katsina.
A cewar rundunar, binciken farko da aka yi wa waɗanda ake zargin ya nuna cewa suna da alaƙa da wani da ake zargin jagoran ’yan ta’adda ne mai suna Mannori.
An ci gaba da tsare waɗanda ake zargin domin gudanar da ƙarin bincike.
Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin ƙoƙarin da take ci gaba da yi na ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, tarwatsa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda da kuma hana su samun damar gudanar da ayyukansu a yankunan da take gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.
Rundunar ta yaba wa al’umma bisa goyon bayan da suke bai wa jami’an tsaro, tare da kira gare su da su ci gaba da kasancewa cikin taka-tsantsan, su kuma gaggauta kai rahoton duk wani abu da suke zargin yana da alaƙa da aikata laifi ko ayyukan ’yan ta’adda ga hukumar tsaro mafi kusa.
