Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnonin Arewa shida ne kacal daga cikin 19, suka goyi bayan takarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.
Shettima, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a fadar Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, yayin bikin naɗa Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, sarautar Sardaunan Masarautar Ilorin.
Ya ce Tinubu ya fuskanci adawa mai zafi a lokacin zaɓen 2023, amma hakan bai hana shi ci gaba da neman kujerar shugaban ƙasa ba.
Shettima, ya ce abin da ya faru ya kamata ya zama darasi ga ’yan siyasa, musamman cewa bambancin ra’ayi a siyasa bai kamata ya zama dalilin raba mutane har abada ba.
Ya yi kira ga ’yan siyasar Kwara da su sasanta tsakaninsu bayan zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC, ba tare da la’akari da wanda ya yi nasara ba.
A cewarsa, Tinubu ya tuntuɓi gwamnonin Arewa da ba su goyi bayan takararsa ba bayan zaɓen 2023, inda ya bayyana musu hakan a matsayin misali na kyakkyawan shugabanci.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su yi mulki cikin tawali’u, yana mai cewa mulki na ɗan lokaci ne kuma riƙe da muƙamin gwamnati bai fi sauran mutane.
