Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa Shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, ba ya Abuja ne saboda yana gudanar da wani aikin hukuma, bayan ƙungiyar Obidient Movement ta nemi ƙarin bayani kan inda yake da kuma ayyukan da yake gudanarwa.
Obidient Movement ta nemi INEC ranar Laraba da ta yi bayani kan inda Amupitan yake da kuma ayyukan hukuma da yake gudanarwa, bayan Kwamishiniyar ƙasa ta INEC, Farfesa Rhoda Gumus, ta bayyana a matsayin shugabar riƙo a wani taron hukuma da tawagar Tarayyar Afirka (AU) ta halarta a Abuja.
A cikin wata sanarwa da Mai Gudanar da ƙasa na ƙungiyar, Dakta Yunusa Tanko, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce lamarin ya haifar da tambayoyi kan inda Amupitan yake da kuma dalilin da ya sa ba ya hedikwatar hukumar.
Lamarin ya biyo bayan wani saƙon da INEC ta wallafa a shafinta na ɗ ranar Talata, 15 ga Satumba, inda ta bayyana Gumus a matsayin shugabar riƙo yayin da take karɓar tawagar Kwamitin Binciken Shirye-shiryen Zaɓe da Buƙatun Nijeriya na Tarayyar Afirka.
Tawagar AU, ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Harkokin Wajen Habasha, Demeke Mekonnen, ta ziyarci hedikwatar INEC da ke Abuja a wani ɓangare na duba shirye-shiryen Nijeriya na babban zaɓen 2027.
Gumus Kwamishiniyar ƙasa ce mai ci a INEC, kuma tana cikin jerin kwamishinonin ƙasa da aka bayyana a shafin intanet na hukumar.
Sai dai Tanko ya ce, abin da ke damun ƙungiyar shi ne, a saninsu, babu wata sanarwa a bainar jama’a da ta bayyana lokacin da Amupitan ya miƙa ragamar aikinsa ga Gumus ko dalilin hakan.
ƙungiyar ta buƙaci INEC da ta bayyana inda Amupitan yake, lokacin da ya bar Abuja, dalilin rashin kasancewarsa da kuma wanda ya ba shi izinin tafiya. Ta kuma nemi hukumar ta bayyana ko shugaban ya fita daga ƙasar, kuma idan ya fita, irin ayyukan hukuma da ya gudanar.
Da take mayar da martani kan buƙatar, INEC ta bayyana cewa shugabanta yana wajen Abuja ne domin gudanar da wani aikin hukuma, tana mai cewa yana da ikon ba wani Kwamishinan ƙasa daga cikin hukumar wasu daga cikin nauyin da ke kansa.
Daraktar Ilimantar da Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai ta INEC, Victoria Eta-Messi, ta shaida wa wakilinmu ta hanyar WhatsApp cewa: “Shugaban yana kan wani aikin hukuma ne a wajen Abuja. Yana da ikon miƙa wasu daga cikin ikonsa ga kowane Kwamishinan ƙasa.”
