Bamanga Tukur: Bango ya faɗi

Spread the love

Rasuwar Alhaji Bamanga Mohammed Tukur a ranar 12 ga Satumba, 2026, yana da shekaru 90, ta kawo ƙarshen wani zango a doguwar tafiyar Nijeriya mai cike da sauye-sauye da ƙalubale a fannonin hidimar jama’a, kasuwanci da gina ƙasa. Rayuwar sa ta kasance sadaukarwa ga iyali, al’umma, Jihar Adamawa, Nijeriya da Afrika baki ɗaya, kuma rasuwar sa ta bar giɓi da ba zai kasance mai sauƙin cikawa ba.

An haifi Alhaji Bamanga a ranar 15 ga Satumba, 1935. Ya kasance ɗan kasuwa, ma’aikacin gwamnati, ɗan siyasa, jami’in diflomasiyya kuma dattijon ƙasa mai daraja, wanda aikin sa ya shafe shekaru masu yawa da gwamnatoci daban-daban. Ya riƙe muƙamin Babban Manaja kuma Babban Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) daga 1975 zuwa 1982, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da ɓangaren harkokin ruwa na Nijeriya a wani muhimmin lokaci na cigaban tattalin arzikin ƙasar nan. A shekarar 1983 aka zaɓe shi a matsayin Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, wadda ta ƙunshi jihohin Adamawa da Taraba na yanzu. Daga baya kuma ya zama Ministan Masana’antu daga 1993 zuwa 1995 a lokacin mulkin soji na Janar Sani Abacha, inda ya yi amfani da ƙwazon sa da jajircewar sa wajen gudanar da wannan muƙami.

Gudunmawar sa ba ta tsaya ga aikin gwamnati kawai ba. Ta hanyar kamfanonin sa, wato BHI Holdings da DADDO Group of Companies, ya kafa tarihi a fannonin masana’antu, aikin gona, sufuri da harkokin kasuwanci, inda ya gina kamfanoni da suka samar da ayyukan yi da dama da kuma damar samun cigaba ga dubban ’yan Nijeriya. A matakin nahiyar Afrika kuma, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Afrika a matsayin sa na Shugaban Zartarwa na ‘African Business Roundtable’ kuma Shugaban ‘NEPAD Business Group’. Ya yi fafutukar ganin an bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika, ɓangaren kamfanoni masu zaman kan su da kuma cigaba mai ɗorewa tun kafin irin waɗannan manufofi su zama ginshiƙan manufofin gwamnati.

A fagen siyasa, Bamanga Tukur ya riƙe muƙamin Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa daga Maris 2012 zuwa Janairu 2014. Ko da yake wa’adin sa ya zo ne a wani lokaci mai cike da ƙalubale a tarihin jam’iyyar, ya kasance muhimmin ɗan siyasa a tafiyar dimokiraɗiyyar Nijeriya. Daga baya kuma an naɗa shi Ambasada mai Wakiltar Nijeriya a Ko’ina (Ambassador-at-Large), wanda hakan ya nuna irin amincewar da gwamnatoci daban-daban suka yi da ƙwarewar sa da kuma matsayin sa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Bamanga a matsayin ƙarshen “wani muhimmin babi a tarihin siyasa da tattalin arzikin Nijeriya.” Ya tuna da shi a matsayin mutum “wayayyen mutum, karami kuma jajirtacce wajen tsare gaskiya da yin hidima,” kuma “mutum ne mai manyan manufofi da ƙarfin gwiwar kasuwanci, wanda ya yi imani da damar da Nijeriya take da ita maras iyaka.” Waɗannan kalmomi, a taƙaice, sun nuna babban ɓangare na gadon da wannan dattijon ya bari domin matasa su nazarta kuma su yi koyi da shi.

Bayan muƙaman da ya riƙe da kamfanonin da ya gina, babban abin da Bamanga Tukur ya gada wataƙila shi ne misalin rayuwar da ya sadaukar wajen hidimar jama’a. A lokacin da rayuwar jama’a ta zama, sau da yawa, tana da alaƙa da fafutukar neman arzikin kai maimakon sadaukarwa, shekaru da dama da Alhaji Bamanga ya shafe yana hidima a fannonin mulki, kasuwanci, siyasa da kuma taimakon jama’a sun ba ’yan Nijeriya wani abin koyi na jajircewa, ƙwazo da ɗaukar nauyi wanda ya dace shugabannin yanzu da na gaba su yi koyi da shi. Rasuwar sa ta sa Nijeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin ƙwararrun muryoyin ta — kuma ta rasa wani kadarko da ake hawa zuwa wani muhimmin babi na tarihin ta wanda kaɗan daga cikin mutanen da suke raye a yau ne suka san shi kai-tsaye.

Jaridar Manhaja tana miƙa matuƙar ta’aziyyar ta ga iyalan Bamanga Tukur, abokan sa, abokan aikin sa da kuma ɗimbin masoyan sa a Adamawa, Nijeriya da faɗin Afrika. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kurakuran sa, ya karɓi kyawawan ayyukan sa, kuma ya yi sakayya da gidan Aljannatul Firdausi, amin.

By ukarofi

Leave a Reply