2023:Duk gwamnonin APC sun goyi bayan Tinubu – Shettima

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya fayyace kalaman da ya yi kwanan nan kan goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu ya samu daga gwamnonin Arewa kafin ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Shettima ya bayyana cewa, maganarsa kan gwamnonin Arewa shida da suka yi imani da Tinubu tare da mara masa baya tana nufin shawarwari da ƙawancen siyasa da aka gudanar ne kafin zaɓen fidda-gwanin shugaban ƙasa na APC da aka gudanar a watan Yuni 2022, amma a yayin gudanar da babban zaɓen ƙasa duka gwamnonin jam’iyyar ne suka mara wa Tinubu baya.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce maganar ba tana nufin matsayin gwamnonin APC na Arewa bayan Tinubu ya samu tikitin takarar jam’iyyar ba, kuma ba ta kasance wata tambaya ko shakku kan irin gudunmawar da suka bayar wajen yaƙin neman zaɓe da nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.

A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar ranar Alhamis, an ce gwamnonin APC na Arewa sun haɗa kai wajen mara wa Tinubu baya bayan kammala zaɓen fidda-gwanin jam’iyyar.

“Bayan zaɓen fidda-gwani, gwamnonin APC a Arewa sun haɗa kai wajen mara wa ɗan takarar jam’iyyar baya, tare da taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓe da ƙoƙarin zaɓe wanda ya kai ga nasarar Shugaba Tinubu a babban zaɓen 2023,” in ji sanarwar.

Shettima ya kuma bayyana girmamawarsa ga gwamnonin Arewa da sauran shugabannin APC, yana mai amincewa da irin gudunmawar da kowannensu da kuma tare suka bayar wajen nasarar jam’iyyar da kuma fitowar Tinubu a matsayin Shugaban ƙasa.

Ya ce ya yi nadamar duk wata fahimta da kalamansa na baya suka haifar wadda za ta iya nuna cewa yana rage ko musanta irin gudunmawar da gwamnonin Arewa suka bayar.

A cewar sanarwar, wannan karin bayani an yi shi ne domin sanya kalaman Mataimakin Shugaban ƙasa cikin yanayin da ya dace da abin da yake nufi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Shettima yana jin daɗin irin ƙwarewar kafafen yaɗa labarai na Nijeriya da kuma yadda suke hulɗa da ofishinsa, tare da roƙonsu da su ci gaba da tabbatar da sahihancin bayanai da kuma bayyana cikakken mahallin kalaman jami’an gwamnati, musamman yayin da ƙasar ke gab da shiga wani sabon yanayin siyasa.

ƙarin bayanin ya zo ne kwana guda bayan da Shettima ya yi jawabi a fadar Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, yayin bikin naɗa Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, sarautar Sardaunan Ilorin.

A wannan jawabin ne Shettima ya ce daga cikin jihohin Arewa 19, gwamnonin shida ne suka yi imani tare da mara wa Tinubu baya. Ya kuma ce Tinubu ya yafewa sauran gwamnonin da ba su mara masa baya ba bayan zaɓen 2023.

Sai dai sabon bayanin da ofishinsa ya fitar ya takaita batun gwamnonin shida ne ga lokacin shawarwari da ƙawancen siyasa da suka gudana kafin zaɓen fidda-gwanin APC na Yuni 2022, yana mai cewa bayan Tinubu ya samu tikitin jam’iyyar, gwamnonin APC na Arewa sun mara masa baya a yaƙin neman zaɓe da kuma ƙoƙarin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.

By ukarofi

Leave a Reply