
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa kwamitin mutane 14 na bincike kan ainihin abin da ya sabbaba harin Sheikh Musa Lukuwa a masallacinsa da ke Mabera, ɗaliban malamin sun nuna rashin gamsuwarsu kan malaman da aka sanya acikin kwamitin.
Manhaja ta ruwaito cewa, ɗaliban sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon zargin cewa wasu daga cikin mambobin kwamitin dama can ba sa tare da shehin akan wasu matsalolin addini don haka akwai yiwuwar su ɗauki ɓangare yayin bincike ko fitar da sakamako akan al’amarin.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai aka kai wa Sheikh Lukuwa hari a masallacinsa na Mabera jim-kaɗan bayan kammala sallar Juma’a, lamarin da ya haifar da fargaba a yankin. Saidai, an yi zargin masallatan da ke wajen sun kama tare da halaka wanda ya kai farmakin.
Bayan aukuwar lamarin ne gwamnatin jihar a umarci a rufe masallacin nasa tare da kafa wani kwamitin malamai da zai gudanar da binciken kan matsalolin addini masu alaƙa da al’amarin akan malamin.
Kwamitin, wanda Sarkin Malamai, Malam Yahya Na Malam Boyi yake jagoranta, an ba shi mako ne biyu domin ya fitar da matsayar shari’a kan matsalolin da ake da saɓani da Sheikh Lukuwa akansu tare da bai wa gwamnatin shawarar matakin da ya kamata a ɗauka a kai.
Sauran malaman sun haɗa da Malam Muhammad Isah Mafara, Malam Bello Na Malam Boyi, Farfesa Mansur Ibrahim, Farfesa Mansur Ibrahim Sa’id. Akwai kuma wakilan Izala daga Kaduna da Jos, da Tijaniyya da Ƙadiriyya, sai kuma na Jama’atu Nasril Islam, majalisar sarkin Musulmi; Kwamishinan harkokin addini, Malam Lawal Maidoki, da kuma Barista Gandi Umar Muhammad a matsayin sakatare.
Da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, babban ɗalibin Malamin, Sheikh Murtala Assada, ya ce mabiyan malamin ba su gamsu da haɗin da aka yi wa kwamitin ba, inda ya ce wasu daga cikinsu suna da saɓanin fahimta da shehin kan ganin wata da koyar da wani Hadisi a yayin karantarwarsa, waɗanda wasu ke fassarawa a matsayin rashin girmamawa ga iyayen Annabi Muhammad (SAW). Ya ce, wannan al’amari ya dace a koma fagen nazarin malamai a madadin kai wa malamin farmakin neman rayuwarsa, yana mai cewa muddin ana son yin adalci, sai a kira zama tsakanin Sheikh Lukuwa da malamai domin su tattauna ta ilimi.
Sheikh Assada ya kuma ƙalubalanci matakin rufe masallacin shehin nasu, inda ya ce karantarwar addini a wajen ba ta bayar da damar ɗaukar irin wannan mataki ba, yana mai zargin gwamnatin jihar da ɗaukar matsaya ba tare da kwamitin ya fara aiki ba. Kazalika, ya yi kira ga mahukuntan da su riƙa warware matsalolin addini ta hanyar tattaunawa ta ilimi daga ɓangaren malamai.
