Daga AISHA ASAS
Littattafai 13 ne aka sanya cikin dogon jerin masu neman lashe babbar lambar yabo ta Baillie Gifford Prize for Nonfiction ta shekarar 2026, wadda ke daga cikin fitattun lambobin yabo da ake bai wa marubutan littattafan da ba na almara ba a Birtaniya.
Cikin littattafan da aka zaɓa akwai Baldwin: ‘A Love Story na Nicholas Boggs’, ‘Stay Alive’ na Ian Buruma, ‘Murder in Paris ’68’ na Edward Chisholm da ‘Days of Love and Rage’ na Anand Gopal. Haka kuma jerin ya ƙunshi ‘Ukrainian Lessons’ na Charlotte Higgins, ‘London Falling’ na Patrick Radden Keefe da ‘Redwood’ na Ben Macintyre.
Sauran littattafan da suka shiga jerin su ne ‘The Nord Stream Conspiracy’ na Bojan Pancevski, Aleɗander na Edmund Richardson, ‘Hotel Eɗile’ na Jane Rogoyska, ‘Never Say War’ na Åsne Seierstad, ‘The Great Dictator’ na Matthew Sweet da ‘The Traveller’ na Andrea Wulf.
Littattafan sun taɓo batutuwa daban-daban, daga tarihi da yaƙi zuwa siyasa, leƙen asiri da rayuwar fitattun mutane. Hakan ya sa gasar ta wannan shekarar ta zo da littattafan da suka bambanta sosai ta fuskar batutuwa da salon binciken marubutansu.
Yanzu littattafan 13 ɗin ne za a tantance kafin a rage su zuwa jerin ƙarshe, inda daga bisani za a zaɓi wanda zai lashe kyautar.
.
