NLC ta koka kan hauhawar farashin fetur a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta amincewa da tallafin gaggawa a matsayin matakin rage raɗaɗi ga ma’aikata a faɗin Nijeriya da raba ɗanyen mai ga matatun gida a farashin naira domin daƙile tasirin hauhawar farashin dangogin fetur a ƙasar.

Haka kuma, cibiyar ƙwadagon ta kuma kirayi gwamnatin da ta faɗaɗa girman rumbunan ajiya na ƙasa domin buƙatar agajin gaggawa da ƙarfafa tsaron makamashi.

A wata sanarwa da Shugaban NLC, Joe Ajaero ya fitar, ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin fetur ka iya haifar da ƙamarin matsin tattalin arziƙi da ‘yan Nijeriya suke fuskanta. Bincike ya nuna cewa, a yanzu ana siyar da litar fetur a gidajen mai akan Naira 1,430 a manyan biranen Nijeriya, inda a wasu wurare ake samu a farashi sama da haka.

A sanarwar, wadda aka yi wa take da “Save the Situation Now”, ƙungiyar ƙwadagon ta yi ƙalubale cewa mai ya sa gwamnatin da ke neman a sake zaɓar ta a nan da wasu ‘yan watanni, take zuba wa ‘yan kasuwa ido wajen cigaba da jefa talaka cikin matsi da suna daidaita gudanarwa.

Ya bayyana cewa, babu wata matsala akan gwamnati muddin ta samar wa al’umma hanyoyin rage musu raɗaɗi musamman a irin wannan hali da ake ciki na buƙatar agajin gaggawa. Kazalika, ya ce matuƙar aka samu ƙarin farashin sufuri, to hakan ka iya shafar na abinci, haya, kuɗin makaranta da wasu buƙatu na yau da kullum a sassan ƙasar.

Akan hakan ne ya yi kira ga gwamnatin tarayyar da ta gaggauta samar da matakan rage raɗaɗi ga magidanta da ƙananan ‘yan kasuwa daga tasirin hauhawar farashin fetur.

By Babaji

Leave a Reply