Marubucin Najeriya ya shiga jerin ƙarshe na masu fafatawa a gasar Caine Prize

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Marubuci ɗan Najeriya Akinwande Remilekun Jordan na cikin marubuta biyar da aka tantance zuwa jerin ƙarshe na Caine Prize for African Writing ta shekarar 2026.

Jordan ya shiga gasar ne da gajeren labarinsa mai suna ‘So Long Now It’s Starting To Look Like Eternity’, wanda aka wallafa a cikin kundin labarai A House That’s Not A Home.

Shi ne kaɗai ɗan Najeriya da ya shiga jerin ƙarshe na bana, yayin da sauran marubutan huɗun suka fito daga Kenya, Kamaru, Masar da Zimbabwe. Su ne Gladwell Pamba, Melara Mvogdobo, Yasmine Zohdi da Simbarashe Steyn Kundizeza.

Caine Prize, wadda ake bai wa fitaccen gajeren labari na marubucin Afirka, ta ce labaran biyar da aka zaɓa sun bambanta wajen salo da jigo, kuma sun fito da ƙwarewa ta musamman wajen ba da labari. A bana an zaɓi waɗannan labaran ne daga cikin sama da 400 da aka gabatar domin gasar.

Editocin labarin Jordan, Haliru Ali Musa da Kingsley Alumona, sun bayyana cewa abin da ya fara ja hankalinsu shi ne irin harshen da ya yi amfani da shi da kuma yadda labarin ya tafiyar da mai karatu zuwa wani yanayi da ba kasafai ake ganin irinsa ba.

Wanda ya lashe gasar zai samu kyautar fam 10,000, yayin da kowane marubucin da ya shiga jerin ƙarshe zai samu fam 500.

By ukarofi

Leave a Reply