Adadin waɗanda suka rasu sakamakon gubar giya ya kai 49 yayin da aka samu 170 a Ondo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar shan wata giya da aka yi zargin an sanya wa guba a wasu ƙauyukan Jihar Ondo ya ƙaru zuwa 49 yayin da aka samu rahoton mutum 170 da al’amarin ya shafa.

A ranar 5 ga Satumba, 2026 ne aka fara samun rahoton al’amarin a garin Odigbo da Araromi Obu da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo bayan mazauna yankunan sun sha wata giyar gargajiya. An ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da suka sha giyar suna tsinci kansu a halin rashin sanin inda suke gabanin su rasu a wurare daban-daban.

A ranar 13 ga Satumba ne gwamnatin Ondo ta sanar da haramta siyarwa da raba nau’ukan giya da ba a tantance su ba da wasu sinadarai bayan mutuwar mutum 30 a jihar. Daga bisani rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wani mai suna Oloruntoba Babatunde bisa zargin sa da samar da sinadaran giya masu cutarwa.

Da yake ganawa da manema labarai a ranar Laraba, Kwamishinan Lafiya na Jihar Ondo, Banji Ajaka, ya ce a yanzu an samu ƙarin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar aukuwar lamarin bayan samun wasu rahotanni a Ƙaramar Hukumar Irele.

Ajaka ya ce mutane takwas ne suka rasu a ƙaramar hukumar a ranar Talata, wanda hakan ya sa jimillar waɗanda suka rasu ta kai 49. Ya bayyana cewa, an kuma samu rahoton jimillar mutum 170 da iftila’in ya shafa idan aka haɗa da waɗanda suka rasu da masu karɓar magani.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, ainihin abin da ya sabbaba gubar giyar shi ne shan sinadarin “ethanol” da mutanen suka yi a cikin abin mayen, yana mai cewa gwamnatin jihar tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta daƙile cigaba da yaɗuwar annobar zuwa sauran ƙananan hukumomin jihar.

By Babaji

Leave a Reply