‘Yan sanda sun ceto mata uku da jaririya a hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘tan sanda sun sami nasarar ceto mata uku da jaririya daga hannun tan bindiga a ƙaramar hukumar Dutsinma na Jihar Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanar haka yace an kwaci bindiga ƙirar AK 47 guda ɗaya ɗauke da harsashi guda biyar.

Ya bayyana cewa bayan samun bayanin sirri na ‘yan bindiga da suka garkuwa da waɗannan mata a kayan makwanta akan iyakar Dutsinma da Ɗanmusa,”shugaban yan sanda na Dutsinma da jami’an sa suka mamaye ƙauyen,” Inji DSP Abubakar Sadiq.

Yan sanda sun sami nasarar ceto waɗannan mata da jaririya bayan da su kai ɗauki ba daɗi da yan bindiga a ƙauyen da ta kai ‘yan bindigan suka gudu suna ɗauke da raunuka na harbin bindiga.

Mata da aka ceto sun haɗa da Marawiya Musa yar shekara 14 da Kariya Ibrahim yar shekara 50 sai Amina Ibrahim yar shekara 21 da jaririya.

Haka kuma DSP Abubakar Sadiq ya ce ‘yan sanda sami nasarar ƙwatar bindiga ƙirar AK 47 mai ɗauke da harsashi da wayar hannu kirar ‘TECNO’ guda ɗaya.

Akwai kuma MP3 player guda uku da ƙunshi uku na tabar wiwi da wuƙa guda ɗaya.

CP Ali Umar Fage ya jinjina wa hami’an sa bisa yadda suka nuna ƙwarewa da basira wajen ceto waɗannan mata.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su rinƙa sa ido da kuma kai rahoto ga ‘yan sanda inda maɓoyar waɗannan ‘yan ta’adda ya ke.

By ukarofi

Leave a Reply