
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar tsaron al’umma ta Cibil Defense (NSCDC) reshen Jihar Neja, ta tabbatar da mutuwar wasu daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa doka ba waɗanda aka kama su yayin wani atisaye a yankin M.I. Wushishi da ke ƙauyen Lukoto a jihar.
An kama su ne yayin wani “atisayen fallasa” da jami’an hukumar suka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026 a matsayin wani ɓangare na hana haramtattun ayyukan haƙar ma’adinai a jihar.
A sanarwar da rundunar da fita a Neja ta hannun Kwamandanta Suberu Aniviye, ta ce atisayen ya yi sanadiyyar kama mutane da dama da hannun haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙwato wasu hujjojin tabbatar da aikata laifi.
Saidai, hukumar ta ce, an samu gawar wasu daga cikin mutanen a komarta a safiyar ranar Alhamis, 17 ga Satumba, bayan abin da ta bayyana a matsayin ɓarkewar wata cuta. A cewar sanarwar, an garzaya da gawarwakin mamatan zuwa Babban Asibiti a Minna domin nazari kan ainihin abin da ya sabbaba mutuwarsu.
Hukumar ta bayyana cewa, tana aiki tare da wasu hukumomin tsaro domin kula da halin tare da kira ga iyalan mamatan da ɗaukacin al’umma da su kwantar da hankali tare da kauce wa matakan da suka saɓa wa doka da oda. Kazalika, ta jaddada aniyarta ta bai wa ‘yancin ɗan-adam kariya da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma gami da kadarorin ƙasa da ababen more rayuwa.
