Idan aka kawo hujjar na bar bashi a Anambara zan daina yaƙin neman zaɓe – Peter Obi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya musanta zargin cewa gwamnatinsa ta bar bashi da wasu basussuka bayan ya kammala wa’adinsa na mulki a jihar.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 15 ga Satumba 2026, yana mayar da martani kan zargin Gwamnatin Jihar Anambra cewa gwamnatinsa ta gada basussuka da suka haɗa da bashin muhalli na Naira biliyan 2, basussukan ’yan kwangila da kuma albashi, garatuti da fansho da ba a biya ba.

Gwamnatin Jihar Anambra ta ce gwamnatin Gwamna Charles Soludo na ci gaba da biyan wasu basussuka da sauran nauyin kuɗi da gwamnatocin baya suka bari, ciki har da waɗanda suka samo asali daga gwamnatocin Peter Obi da tsohon Gwamna Willie Obiano.

Sai dai Obi ya ce gwamnatinsa ta biya basussukan garatuti da sauran basussukan da aka tara tsawon shekaru, waɗanda suka haura Naira biliyan 35, kafin ta miƙa mulki.

Ya ƙara da cewa a lokacin da ya miƙa mulki, jihar ba ta bin ma’aikata, ’yan fansho ko ’yan kwangila waɗanda suka kammala ayyukansu kuma aka tabbatar da ingancinsu.

“Mun biya basussukan garatuti da sauran basussukan da aka tara tsawon shekaru, waɗanda suka haura Naira biliyan 35. A lokacin miƙa mulki, jihar ba ta bin kowa albashi, garatuti ko fansho, haka kuma ba ta bin wani ɗan kwangila da ya kammala aikin da aka ba shi kuma aka tabbatar da shi,” inji Obi.

Ya kuma yi bayani kan ce-ce-ku-ce da ya shafi Naira biliyan 2 na kuɗin muhalli da aka ware domin magance matsalar zaizayar ƙasa a Oko/Umuchiana.

Obi ya ce an saki kuɗin ne kimanin watanni uku kafin ƙarshen wa’adinsa, amma ya ƙi matsin lambar da aka yi masa na kashe kuɗin kafin ya bar mulki, saboda an ware su ne domin wani takamaiman aiki.

Ya ce ya bar kuɗin ga gwamnatin da za ta gaje shi ne saboda, a cewarsa, gwamnati abu ce mai ci gaba, kuma kuɗin an ɗaure su ne da aikin da aka ware su domin aiwatarwa.

Obi ya ce an bar kuɗin ba tare da an taɓa su ba a wani asusun First Bank, inda ya ce akwai sama da Naira biliyan 2.13 a cikin asusun.

“Kuɗin muhalli na Naira biliyan 2 da ake magana a kai an saki su ne watanni uku kacal kafin ƙarshen wa’adina domin magance matsalar zaizayar ƙasa ta Oko/Umuchiana. Duk da matsin lambar da aka yi na a kashe kuɗin, na ƙi, saboda na dage cewa a bar su ga wanda zai gaje ni, domin gwamnati abu ce mai ci gaba kuma an ware kuɗin ne domin wani takamaiman aiki.

“Saboda haka, an bar kuɗin gaba ɗaya a asusun First Bank, inda akwai sama da Naira biliyan 2.13.

“Yana da muhimmanci a bayyana cewa kuɗaɗen da aka ware domin wasu takamaiman ayyuka ko wasu dalilai ba su ma cikin sama da Naira biliyan 75 da muka bari a matsayin ajiya,” in ji shi.

Obi ya ƙalubalanci duk wanda ke da hujjar da ta saba da bayanansa da ya fito da ita, yana mai cewa zai daina yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa idan aka tabbatar da cewa ya bar basussukan da ake zarginsa da su.

“Idan wani zai iya tabbatar da wani abu da ya saba da wannan, zan daina yaƙin neman zaɓe,” in ji Obi.

Sai dai cece-kuce kan matsayin kuɗaɗen Anambra da basussukan da aka gada ya daɗe yana gudana tsakanin Obi da masu sukar bayanan gwamnatinsa. Gwamnatin Anambra ta ce har yanzu ana cire wasu kuɗaɗe daga rabon jihar na wata-wata domin biyan basussukan da gwamnatocin baya suka ci, yayin da ta ce gwamnatin Soludo ba ta karɓi sabon bashin bankin kasuwanci ba tun bayan hawanta mulki.

By ukarofi

Leave a Reply