Daga DAUDA USMAN a Legas
Rahotanni sun nuna cewa, almajirai da mabarata masu yawa daga wasu jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya na ci gaba da zuwa Jihar Ogun domin gudanar da sana’ar bara, wadda suka mayar da ita hanyar neman abincin yau da kullum.
Alhaji Sabiu Ya’u Mohammed, ɗan asalin Jihar Borno, wanda shine Sarkin Yaƙin Masarautar Mai Martaba Sarkin Al’ummar Hausawa mazauna ƙaramar Hukumar Iperu da ke Jihar Ogun, kuma Kwamandan ’Yan Sintiri a garin Ogere, ya nuna rashin jin daɗinsa kan wannan lamari.
A yayin da yake zantawa da Blueprint Manhaja a garin Ogere, Sarkin Yaƙin ya ce almajirai da mabarata, maza da mata, suna zuwa ne daga wasu jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya, inda ya ce ’yan asalin Jihar Katsina suka fi yawa.
Ya ce, wasu daga cikinsu na zuwa da aananan yara, waɗanda shekarunsu ba su wuce biyar zuwa shida ba, inda suke ɗaukar su a manyan motoci su zo garin Ogere domin yin bara da neman abin da za su ci.
Sarkin Yaƙin ya ce abin da ya fi ba shi takaici shi ne yadda wasu daga cikin matan mabaratan da ya yi wa tambayoyi kan ƙananan yaran da suke zuwa da su suka bayyana cewa, maimakon su kai yaran makaranta domin neman ilimin boko da na addinin Musulunci, sai suke zuwa da su wajen bara.
Ya ce, abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ake barin yaran cikin mawuyacin hali, tare da rayuwa ba tare da samun ingantaccen ilimi ba.
Ya ƙara da cewa, a mafi yawan lokuta, mabaratan ba su san inda suka fito ba, abin da ke sa idan wani abu ya faru, a rasa wanda za a kira domin sanar da shi.
Sarkin Yaƙin ya ce kwanan nan wata yarinya ta rasu kuma aka yi mata jana’iza, amma har yanzu ba a gano iyayenta ba.
Da yake ci gaba da bayyana masa damuwar, ya ce ya sake tambayar wasu daga cikin mabaratan game da ƙananan yaran da suke zuwa da su, inda suka ce yaran ba nasu ba ne.
A cewarsu, iyayen yaran suna can gida, kuma suna ba su yaran ne domin su zo su nemi kuɗi. Idan suka koma gida, sai su biya iyayen yaran wani kaso daga cikin kuɗin da suka samu.
Sarkin Yaƙin Ogere ya bayyana wa Jaridar Blueprint Manhaja cewa wasu daga cikin matan da ke bara ba almajirai ba ne, kuma wasu daga cikinsu suna da mazajen aure, amma sun bar mazajensu a gida suka zo Ogere domin neman kuɗi.
Saboda haka, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa da sauran shugabanni da su duba wannan lamari da muhimmanci, domin kare rayuwar ƙananan yaran da ake kai wa bara.
Ya ce, ya kamata shugabanni su dubi Allah da ManzonSa wajen nemo mafita ga matsalar, domin yaran da ake kai wa bara na girma ne ba tare da samun ilimin boko ko na addinin Musulunci ba.
Sarkin Yaƙin ya kuma bayyana cewa akwai wani attajiri a Kano da ake kira Mai Kifi, wanda ke da tankokin ajiyar man fetur, wanda bayan ya samu labarin halin da yaran suke ciki, ya zo ya yi hayar motoci domin mayar da su jihohin da suka fito.
Ya yi addu’ar Allah Ya saka wa attajirin da mafificin alheri bisa wannan mataki da ya ɗauka.
A ƙarshe, ya yaba wa Gwamnan Ogun bisa gudunmawar da yake bayarwa ga Hausawa mazauna jihar da kewaye, yana mai cewa irin wannan goyon baya na taimakawa wajen kyautata zaman tare tsakanin al’ummomin jihar.
