Muna da tabbacin NDC za ta yi nasara a zaɓe mai zuwa — Umar Auwal

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An bayyana cewa jam’iyyar NDC za ta iya samun nasara a zaɓe mai zuwa, sakamakon abin da wasu ’yan jam’iyyar suka bayyana a matsayin mawuyacin halin da jam’iyya mai mulki ta jefa ƙasar a ciki.

Shugaban ƙungiyar Masu Tallata ɗan Takarar Sanatan Kano ta Kudu, Hon. Kasim Ibrahim Batayya, Kwamared Umar Auwal Unguwar Dubu, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a wajen tantance ’yan ƙungiyar da aka gudanar a ɗakin taro na Hafizun Event Center cikin satin da ya gabata.

Ya ce dalilin yin rajistar ’yan ƙungiyoyin shi ne domin sanin adadinsu da kuma irin gudunmawar da suke bayarwa wajen tafiyar ɗan takarar, da kuma ƙoƙarin tabbatar da nasarar jam’iyyar NDC a dukkan zaɓukan da ke tafe.

“Muna shirya wannan taro ne domin haɗa kan masu tallata ’yan takararmu a kafafen sada zumunta, domin mu san yawansu da irin gudunmawar da suke bayarwa a wannan tafiya. Domin idan Allah ya ba mu nasara, mu san irin taimakon da za mu yi musu,” inji Umar Auwal.

Ya kuma bayyana ɗan takarar kujerar Sanata, Hon. Kasim Ibrahim Batayya, a matsayin mutum mai cika alkawari, yana mai cewa hakan ne ya sa wasu daga cikin al’umma ke fatan samun nasararsa domin ya kawo ayyukan ci gaba a yankunansu.

Umar Auwal ya sake bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar NDC za ta samu nasara a zaɓe mai zuwa.

Shi ma da yake nasa jawabin ga ’yan ƙungiyoyin, Hon. Kasim Ibrahim Batayya, ya nuna jin daɗinsa da yadda ’yan ƙungiyoyin ke yaɗa manufofinsa da kuma shirye-shiryen ayyukan ci gaba da yake cewa zai kawo idan ya samu nasara.

Ya ce masu tallata ’yan takara suna taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa manufofi da manufofin ’yan takara tun kafin samun nasara.

Batayya ya kuma tabbatar wa ’yan ƙungiyoyin cewa a shirye yake ya tafi tare da su kafada da kafada idan ya samu kujerar, bisa la’akari da gudunmawar da suke bayarwa wajen tafiyar tasa.

A yayin rajistar, an yi wa kusan mutane 1,000 rajista domin tantance adadinsu da kuma fahimtar yadda suke gudanar da ayyukansu na tallata ’yan takara da jam’iyyar, daga matakin ɗan takarar shugaban ƙasa zuwa ’yan takarar gwamna, Sanata, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin jiha.

Taron ya samu halartar ’yan ƙungiyoyin daga ƙananan hukumomi 15 na yankin.

By ukarofi

Leave a Reply