Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Shugaban Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ’Yan Tifa ta ƙasa, reshen jihar Kano, Kwamared Isah Jafar Kofar Na’isa, ya ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar na shiyyoyi daban-daban da ke jihar Kano.
An gudanar da ƙaddamar da shugabannin ne ranar Asabar da ta gabata, inda Kwamared Kofar Na’isa ya ja hankalinsu da su kasance masu bin doka da oda a yayin gudanar da sana’arsu, tare da kasancewa masu kawo abubuwan da za su taimaka wajen ci gaban ƙungiyar.
Kwamared Kofar Na’isa ya ce a ranar da aka gudanar da ƙaddamarwar ne ya cika shekara guda da fara jagorantar ƙungiyar, yana mai cewa tun bayan hawansa an samu gagarumin ci gaba.
Ya ce daga cikin nasarorin da aka samu akwai daidaita harkokin kuɗaɗen shiga na ƙungiyar, tallafa wa ’yan ƙungiyar da ke fama da rashin lafiya, da kuma samar da kyakkyawar fahimta tsakanin ’yan ƙungiyar da jami’an tsaro, har ma da ƙara wa sunan ƙungiyar martaba a wuraren da ba a san ta a baya ba.
Ya yi kira ga ’yan ƙungiyar da su riƙa halartar tarukan da ƙungiyar ke gudanarwa, domin hakan zai ba su damar sanin halin da ƙungiyar take ciki da kuma ayyukan da shugabanninta suke gudanarwa domin ci gabansu da kuma ci gaban sana’ar da suke yi.
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Adewale Aliu Mayungbe, wanda mataimakinsa, Kwamared Mamunu Ibrahim Takai, ya wakilta, ya ce babban aikin da ke gaban ’yan ƙungiyar ya ta’allaka ne kan abubuwa biyu.
Ya ce na farko shi ne kare haƙƙin ɗan ƙungiya, ta yadda ba za a bari wani mutum ko wasu mutane su cutar da shi ba, yayin da na biyu shi ne kare haƙƙin sauran al’umma, ta yadda ba za a bari wani ɗan ƙungiya ya cutar da sauran jama’a ba.
Ya kuma bukaci ’yan ƙungiyar da su bai wa gwamnati da jami’an tsaro haɗin kai yayin gudanar da ayyukansu.
Haka kuma, ya yi kira gare su da su girmama tsofaffin shugabannin da suka gada, tare da neman shawarwarinsu domin tabbatar da dorewar shugabanci da kuma ci gaban ƙungiyar.
Su ma waɗanda aka rantsar sun bayyana farin cikinsu, tare da ɗaukar alkawarin gudanar da shugabancinsu cikin taimakon ’yan ƙungiya da yin aiki kafada da kafada da sauran shugabannin jihar da na ƙasa.
An gudanar da taron a ɗakin taro na Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Kano, inda shugabannin ƙungiyar daga sassa daban-daban na jihar suka halarta, tare da wakilan Ma’aikatar Sufuri, Ma’adanai da sauran ƙungiyoyin da ke da alaƙa da harkokin sufurin.
