Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Sabon Sarkin Fawa na Babbar Mayankar Kasuwar ’Yan Awaki da ke ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano, Alhaji Ahmad Musa, ya bayyana cewa tun bayan hawansa kujerar ya gudanar da wasu ayyukan ci gaba tare da samar da hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a mayankar.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa da ke cikin kasuwar ranar Asabar.
Alhaji Ahmad ya ce an samu nasarorin ne sakamakon haɗin kai da goyon bayan da al’ummar kasuwar suke bai wa masarautarsa, yana mai cewa tun kafin hawansa kan kujerar Sarkin Fawa, ’yan kasuwar suka fara ƙoƙarin magance matsalar shaye-shaye da kuma kawar da masu yawo ba tare da sana’a ba domin tabbatar da tsaro a wajen sana’ar tasu.
Ya yaba wa ’yan kasuwar bisa yadda suke ba shi goyon baya da kuma shawarwarin da suke bayarwa kan ci gaban kasuwar da sana’ar fawa.
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su kula da mayankar tare da ɗaukar matakan zamanantar da ita kamar sauran takwarorinta da ke wasu jihohin ƙasar, ganin yadda sana’ar ke taimakawa wajen rage yawan marasa aikin yi.
Ya ce suna buƙatar gwamnati ko masu hali su taimaka wajen samar da fitilun zamani masu amfani da hasken rana, da kuma magudanan ruwa a mayankar.
A cewarsa, idan damina ta yi, ’yan kasuwar na fuskantar matsala wajen gudanar da sana’ar saboda rashin magudanan da ruwa zai bi, yayin da rashin haske da dare kuma ke barazana ga dukiyoyin da suke ajiye a wurin.
Daya daga cikin masu gudanar da sana’ar fawa a kasuwar, wanda kuma shi ne sakataren Sarkin Fawa, Shamsideen Muhammad, ya yi kira ga shugabanni da su ziyarci kasuwar domin ganin irin halin da take ciki da idanunsu, tare da samar musu da tallafin da ya dace.
Ya ce tun bayan zuwan sabon sarkin an samu sauye-sauye a mayankar, inda aka samu ci gaba, ciki har da samar da ofishin gudanar da harkokin kasuwar, wanda a baya ba ta da shi.
Ya ƙara bayyana damuwarsa kan yadda kasuwar ke da matuƙar tasiri wajen samar wa matasa ayyukan yi, amma rashin kulawa da wasu muhimman abubuwa na barazanar mayar da ita baya.
Ya ce rashin fitilu na zamani ya tilasta musu rufe kasuwar da zarar yamma ta yi ko kuma su yi amfani da fitilunsu na kansu. Haka kuma, rashin magudanan ruwa na hana wasu masu sayen kayan shiga kasuwar a lokacin da aka yi ruwa.
