Daga RABIU SANUSI a Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada ƙudirinta na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da al’ummar Sinawa da ke zaune a jihar, tare da tabbatar wa ’yan ƙasashen waje da masu zuba jari cewa za ta ci gaba da kare rayukansu, dukiyoyinsu da harkokin kasuwancinsu na halal.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, SFIPMA, MNIM, MNIPS, MASIS, ya bayyana hakan ne ranar Talata, 15 ga Satumba, 2026, lokacin da ya karɓi Mr. Ni Zhichen daga Sashen Hulɗa da Jakadanci na Ofishin Jakadancin Sin da ke Abuja, wanda ya kai wa rundunar ziyarar ban girma a hedikwatarta da ke Bompai, Kano.
Manufar ziyarar ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Rundunar ’Yan Sandan Kano da al’ummar Sinawa da ke jihar da kuma Nijeriya baki ɗaya, musamman a fannonin tsaro, yaƙi da laifuka, musayar bayanan sirri da kare rayuka da dukiyoyin masu zuba jari.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Mr. Ni Zhichen ya ce al’ummar Sinawa da ke Kano na ci gaba da faɗaɗa harkokinsu na kasuwanci, ciniki da zuba jari, lamarin da ya sa samun haɗin gwiwa mai ɗorewa da hukumomin tsaro ke da muhimmanci wajen tabbatar da tsaron rayuka da jarin kasuwanci.
Ya nuna godiyarsa bisa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin al’ummar Sinawa da Rundunar ’Yan Sandan Kano, tare da yaba wa zaman lafiyar da ake samu a jihar.
Ya ce, “Mun zo Kano ne saboda Kano jiha ce mai matuƙar zaman lafiya. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka zaɓi zama a Kano. Mun kuma zaɓi Kano saboda wadata da tsaro da ke jihar. Muna da yaƙinin cewa da taimakon ’yan sanda, ’yan ƙasarmu da jarinsu za su ci gaba da kasancewa cikin aminci.”
A nasa jawabin, CP Bakori ya tarbi tawagar Sinawa, tare da tabbatar musu cewa Kano gida ce ga al’ummar Sinawa da sauran ’yan ƙasashen waje.
Ya bayyana mutanen Kano a matsayin masu karamci da son zaman lafiya, yana mai cewa rundunar ta himmatu wajen samar da ingantaccen tsaro domin bunƙasar kasuwanci da zuba jari na halal.
Kwamishinan ya kuma bayyana irin shirye-shiryen da rundunar ke yi gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ya tabbatar da cewa ana ɗaukar matakan tsaro da suka dace domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana da tsari.
Ya ce rundunar na aiki tare da sauran hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki domin dakile tashin hankali da tabbatar da doka da oda kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.
A yayin tattaunawar, ɓangarorin biyu sun duba fannonin da za su amfana da haɗin gwiwa, waɗanda suka haɗa da horar da jami’an tsaro, inganta fasahar aikin ’yan sanda, musayar bayanan sirri, yaƙi da laifuka da kuma kyautata hulɗa da al’umma.
CP Bakori ya jaddada muhimmancin amfani da fasahar zamani wajen aikin ’yan sanda da musayar bayanai a kan lokaci domin magance laifukan tattalin arziki da na ƙetare iyakokin ƙasa.
Ya kuma buƙaci al’ummar Sinawa da su ci gaba da bai wa rundunar bayanan da za su taimaka wajen hana aikata laifuka da kuma gaggauta ɗaukar matakan tsaro.
Kwamishinan ya bayyana ziyarar a matsayin muhimmin mataki wajen zurfafa hulɗar diflomasiyya, tattalin arziki da tsaro tsakanin Nijeriya da Sin, tare da tabbatar wa dukkan mazauna jihar, masu zuba jari da baƙi cewa Rundunar ’Yan Sandan Kano za ta ci gaba da kiyaye doka da oda, tare da kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.
