Burina shi ne na taimaka wa al’umma a harkar lafiya — Hassan Dawaki

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU aa Kano

Wani ƙwararren ma’aikacin jinya kuma mai kishin al’umma, Hassan Musa Dawaki, ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da taimaka wa al’umma, musamman a fannin kiwon lafiya.

Dawaki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake buɗe sabon asibitinsa mai suna El-Hassan Clinic and Maternity, da ke garin Tsakuwa a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano, ranar Litinin.

Da yake bayani kan manufar buɗe asibitin, ya ce tun kafin ya samu damar karatu a fannin aikin jinya yake da burin ganin ya samu damar taimaka wa al’umma wajen kula da lafiyarsu.

Ya bayyana farin cikinsa da godiya ga Allah da ya cika masa wannan buri na buɗe asibiti mai zaman kansa domin taimakon jama’a, yana mai cewa manufarsa ita ce ta yi wa al’umma hidima tare da bayar da gudunmawa wajen inganta lafiyar al’umma.

Hassan Dawaki ya ƙara da cewa asibitin ba zai tsaya ne kawai wajen duba mata masu juna biyu ba, illa dai zai samar da wasu muhimman ayyukan kiwon lafiya, ciki har da kwantar da marasa lafiya, yin tiyata, gudanar da gwaje-gwaje da bayar da shawarwari kan harkokin tazarar haihuwa.

Ya ce asibitin zai kuma taimaka wajen gudanar da ayyukan rigakafin wasu cututtuka da gwamnati ke aiwatarwa, domin ƙara inganta lafiyar al’ummar yankin.

Dawaki ya yi kira ga al’ummar yankin da su bai wa ma’aikatan asibitin goyon baya da haɗin kai, domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da tabbatar da dorewar asibitin da kuma ci gaban yankin.

Da suke magana a madadin sauran ’yan uwansu, Alhaji Hussaini Hashim da Usman Musa Usman, sun bayyana jin daɗinsu da ganin wannan aikin alheri da ɗan uwansu ya yi domin ci gaban al’umma.

Sun ce aikin ba zai amfani garin Tsakuwa kaɗai ba, har ma da wasu makusantan yankunan, suna mai cewa matakin ya nuna irin kishin al’umma da Hassan Dawaki yake da shi, musamman a fannin lafiyar jama’a.

Sun kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da bai wa asibitin goyon baya da haɗin kai, tare da ba da shawarwarin da za su taimaka wajen ganin ya dore kuma ya cimma manufofin da aka kafa shi domin su.

Taron buɗe asibitin ya samu halartar Sarkin garin Tsakuwa, Alhaji Isma’il Santali Tsakuwa; Dagatan garin Santolo da Sarai, masu unguwanni, ma’aikatan lafiya, ’yan ƙungiyoyi, ’yan siyasa, ’yan uwa da abokan arziki.

By ukarofi

Leave a Reply