
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu ɓullar wasu sababbin zarge-zarge a game da mutuwar wasu da ake zargin masu aikin haƙar ma’adinai ne ba bisa doka ba a hannun Hukumar Tsaron Al’umma ta Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Neja.
Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta umarci a gaggauta dakatar da Kwamandan hukumar na jihar, Suberu Aniviye da yin cikakken bincike kan al’amarin.
Rahotanni sun nuna cewa, wata majiya daga ofishin NSCDC na Neja da ta nemi a sakaye sunanta, ta yi zargin cewa masu haƙar ma’adinan sun rasu ne sakamakon rashin wadataccen kulawa, ƙarancin iskar numfashi da zafi kasancewar an jibge su a wani waje mara isasshen iska.
A cewarta, ɗakunan rufe masu laifi na iya ɗaukar mutum uku ne zuwa biyar kaɗai saboda ƙarancin iska da tsananin zafi, amma an zuba sama sa mutane 15, inda wasu suke kwanciya akan takwarorinsu. Majiyar ta kuma yi zargin cewa ɗakunan sun kasance cikin yanayi na rashin tsafta da ya kai wasu ma aciki suke fitsari saboda rashin makewayi ga waɗanda aka tsare.
Ta kuma ce, wannan ba shi ne karo na farko ba da ake samun masu laifi suna mutuwa a ofishin, inda ta ce wannan shi ne wanda ya fi ɗaukar hankalin jama’a saboda waɗanda al’amarin ya rutsa da su ba a ɗauke su a matsayin masu babban laifi ba da kuma adadin mace-macen da aka samu.
Wani ɗan uwa ga ɗaya daga cikin mamatan mai suna Lafiagi, ya ce an jibge masu haƙar ma’adinan ne a gurin da dabbobi ma ba za su ji daɗin zama ba ballantana bil’adama. A cewarsa, zafi, matsi da dauɗar da ke wajen ma kaɗai sun isa halakar da mutane cikin sa’o’i, yana mai cewa rashin kulawa sun taimaka wajen sanya su cikin rashin lafiya da mutuwarsu daga bisani.
Wannan al’amari ya janyo zanga-zanga akan hanya a yankin Flamingo Junction da ke Maitumbi a jihar. Kazalika, an yi zargin cewa wani uba mai suna Mallam Abdullahi, ya je babban ofishin hukumar a Minna domin neman belin ɗansa amma ce sai ya biya Naira 500,000
Tuni dai Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci a gaggauta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja, Suberu Aniviye bayan faruwar iftila’in da kuma a yi cikakken bincike a kai.
