
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Peter Obi, ya fitar da rahoton miƙa mulki yayin amsa wa iƙirarin gwamnatin Anambara na cewa ya bar jihar da tarin bashi da wasu nauye-nauyen kuɗaɗe.
Wannan mataki ya sanya rikicin da ke tsakanin Obi da gwamnatin jihar kan bashi da nauyin kuɗi da aka yi zargin an bar wa gwamnatocin baya ya tsananta.
Wani rahoton miƙa mulkin Obi da aka fitar, ya nuna cewa ya bar asusun jihar da rarar kuɗi da adadinsa ya Naira biliyan 86. Kodineta riƙo na Ƙasa na Tafiyar Obi, Dakta Yinusa Tanko ne ya fitar da rahoton miƙa mulkin, wanda ke ɗauke da kwanan wata 17 ga Maris, 2014 a ranar Laraba.
Rahoton ya ƙunshi, bayanai a taƙaice na halin kuɗaɗe da tsohon gwamnan nan Anambara ya bari a ranar da ya miƙa ragamar mulkin jihar.
Wannan taƙaddama ta samo asali ne a lokacin da gwamnatin jihar ta yanzu ta ta yi iƙirarin cewa har yanzu tana cigaba da biyan bashin gwamnatocin da suka gabace ta ciki har da na Peter Obi da Willie Obiano.
Obi ya ƙalubalanci gwamnatin Soludo da ta fitar da hujjar da ke tabbatar da iƙirarin nata cewa ya bar Anambara da tarin bashi akanta. Ya kuma yi iƙirarin muddin aka tabbatar da wannan zargi akansa, to zai ajiye yaƙin neman zaɓen 2027.
Sannan, akan wannan rikici ne ‘yan ɓangaren kare Obi suka fitar da takardar rahoton halin kuɗaɗen jihar a lokacin da tsohon gwamnan yake miƙa mulki, duk da cewa gwamnatin ta yanzu tana cigaba da zama akan iƙirarin bashin da gwamnatocin baya suka tara.

