
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance wayayyu yayin nazari kan siyan hannayen jarin kamfanin Matatar Ɗangote ta (IPOs), yana mai gargaɗin su da kada su siyar da gidajensu ko amfani da kuɗaɗen karatun ‘ya’yansu wajen siyan hannun jari.
Mai Martabar ya yi wannan kira ne a taron wayar da kan jama’a kan hannun jarin FZE IPO na Kamfanin Matatar Ɗangote da dangogin fetur a Jihar Kano, wanda ya tara masu zuba jari, abokan hulɗa, wakilan bankuna, jagororin masana’antu, sarakunan gargajiya da sababbin masu zuba jari.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriyar (CBN) ya kuma shawarci masu niyyar siyan hannun jari da su zuba iya abin da za su iya kamar Naira 10,000, N20,000 ko N30,0000, yana mai gargaɗin su da kada su takura kansu wajen siyar da wasu kadarori domin siyan hannu a kamfanin.
“Kuma ba za ku yi da-na-sani ba, mutane na siya daga ko’ina a ƙasar. Ina magana ne a matsayin Sarkin Kano. Zan so mutanena su zama sune masu mallakar wannan. Ba na so a bar mu a baya a kasuwannin zuba jari,” inji basaraken.
Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar Kano da su tallafa wa “ɗansu”, Aliko Ɗangote wajen siyan hannun jari a kamfanin nasa, yana mai cewa za a sha mamakin yadda ƙaramin kuɗin da aka zuba zai bunƙasa zuwa mai yawa nan da wasu shekaru masu zuwa.
Kazalika, ya yaba wa Ɗangote bisa gudunmawarsa ga harkar tattalin arziƙin Nijeriya, yana mai tunatar da lokacin da yake gwamna a CBN, da ƙalubale masu alaƙa da shigowa da tataccen fetur daga ƙasar waje zuwa Nijeriya.
