An kashe ’yan ta’adda sama da 1,200, an kama masu taimaka musu 758 a arewa maso gabas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, mai barin gado, Manjo Janar Abubakar Abdulsalam, ya bayyana cewa an kwato sama da N350m daga hannun masu ɗaukar nauyin ayyukan ’yan ta’adda tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin rundunar.

News Point Nigeria ta ruwaito cewa kwamandan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, da ke Maiduguri, Jihar Borno, a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin kammala aikinsa a rundunar.

Abdulsalam ya ce lokacin da ya karɓi ragamar rundunar a ranar 28 ga Afrilu na shekarar da ta gabata, hedikwatar sojoji ta ba shi umarni a fili na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas, domin harkokin zamantakewa da tattalin arziƙi su ci gaba.

Ya ce ana auna nasarar wannan manufa ne ta hanyar dawo da muhimman ayyuka, ciki har da sake buɗe kasuwanni, manyan hanyoyin jigilar kayayyaki da makarantu, da kuma dawo da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa garuruwansu na asali.

“Da haɗin kanmu gaba ɗaya, mun ga sama da iyalai 7,000 da suka rasa matsugunansu sun koma garuruwansu na asali, kuma a yau wasu al’ummomin da aka yi shekaru ana watsi da su sun sake zama da mutane,” inji shi.

Ya ƙara da cewa an gano tare da tarwatsa sama da na’urorin fashewa 300 cikin aminci daga ranar 25 ga Afrilu zuwa yanzu.

“Bugu da ƙari, an kwato sama da N350m daga masu ɗaukar nauyin ’yan ta’adda, sannan an kama aƙalla mutane 758 da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda wajen samun kayan aiki da sauran abubuwan da suke buƙata,” inji shi.

A cewarsa, an kuma mayar da sama da mutane 3,000 daga Jamhuriyar Kamaru zuwa Nijeriya bisa radin kansu, cikin tsari mai kyau da mutunci.

Ya ce sansanin horas da matasan da za su yi aikin bautar ƙasa na NYSC ya koma Maiduguri bayan shafe sama da shekaru 13, yayin da jarabawar WAEC da NECO ke sake gudana a wasu al’ummomi kamar Banki da Gwoza.

Ya ƙara da cewa an sake buɗe hanyoyin kasuwanci, yayin da kasuwannin cikin gida suka dawo da harkokinsu.

Abdulsalam ya ce rundunar ta samu nasarori da dama a fagen yaƙi, ciki har da hallaka sama da ’yan ta’addan JAS da ISWAP 1,200, ciki har da wasu manyan shugabanninsu.

“Ya zuwa ƙidayar ƙarshe, an kawar da sama da manyan shugabannin ’yan ta’adda 216,” inji shi.

Ya kuma ce dakarun sun kwato sama da makamai iri daban-daban 500, tare da harsasai sama da 25,000 masu girma da ƙananan ƙarfi iri-iri.

Kwamandan mai barin gadon ya kuma ce rundunar ta fuskanci wani gagarumin ƙaruwar mutanen da ke miƙa wuya a baya-bayan nan, musamman a wannan shekarar.

Ya danganta wannan ci gaba da matsin lambar da sojoji ke ci gaba da yi kan ’yan ta’addan, tare da samar da hanyoyin da ke ba waɗanda suka miƙa wuya damar komawa rayuwa cikin mutunci ta hanyar wasu matakan da ba na yaƙi kai tsaye ba.

Abdulsalam ya yaba wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar OO Oluyede, Babban Hafsan Sojojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, da gwamnatin Jihar Borno bisa irin tallafin da ya samu a lokacin da yake jagorantar rundunar.

Ya ce yana miƙa godiyarsa ta musamman ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa jagorancinsa da kuma matakan da ya ɗauka wajen inganta jin daɗin jami’an tsaro da ƙarfin rundunar wajen gudanar da ayyukan yaƙi.

Ya kuma gode wa Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar OO Oluyede, CFR, bisa jagoranci da kuma taimakawa wajen samar da dabarun haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Haka kuma, ya yabawa Babban Hafsan Sojojin ƙasa, Laftanar Janar W. Shaibu, NAM, saboda ci gaba da ba da umarni da kuma ƙarfafa rundunar da ƙarin dakaru, kayan aiki da sauran abubuwan da ake buƙata domin gudanar da ayyukan yaƙi.

A nasa ɓangaren, Abdulsalam ya gode wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, bisa ci gaba da tallafa wa rundunar, musamman wajen samar da muhimman kayan aikin yaƙi da suka haɗa da motocin MRAP, kyamarorin sa ido masu dogon zango da jiragen sama marasa matuƙa (drones), da sauran kayan aiki.

By ukarofi

Leave a Reply