Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi, wadda ta lashe musabaƙar Alƙur’ani ta duniya a Saudiyya, kyautar Naira miliyan 20.
A makonnin baya-bayan nan ne Maryam, wadda ’yar asalin Jihar Gombe ce, ta lashe Musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Makka, Saudiyya.
A yayin da take karrama ta a Abuja ranar Talata, Uwargidan Shugaban ƙasar ta bayyana nasarar Maryam a matsayin abin alfahari ga Nijeriya da kuma ’yan mata a duniya.
Ta ce Maryam ta zama abin koyi ga matasa, musamman ’yan mata, saboda yadda ta yi amfani da baiwar da Allah Ya ba ta wajen samun nasara a fagen karatun Alƙur’ani.
Ta kuma yaba wa iyayen Maryam, malamanta da masu ba ta horo bisa gudunmawar da suka bayar wajen haɓaka iliminta da baiwarta.
“Maryam ta nuna mana muhimmancin aiki tukuru, da’a da jajircewa,” in ji Remi Tinubu.
Ta kuma shawarci Maryam da ta ci gaba da neman shawarwari da jagoranci daga ƙwararru yayin da take ci gaba da karatunta.
Uwargidan Shugaban ƙasar ta bayyana cewa ilimi na daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ba muhimmanci, musamman samar da dama ga matasa su bunƙasa baiwarsu.
Ta kuma yi alkawarin tallafa wa Maryam wajen neman digiri na gaba.
A nasa jawabin, Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce nasarar Maryam abin alfahari ce ga jihar da Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce Maryam ta samu nasarar ne bayan ta tsallake matakai daban-daban na gasannin Alƙur’ani na cikin gida da na ƙasa kafin ta wakilci Nijeriya a gasar ƙasa da ƙasa.
Maryam ta wakilci Nijeriya ne a gasar karatun Alƙur’ani, haddar Alƙur’ani da tafsiri, inda ta zama ta farko a rukunin mata. Gasar ta bana ta samu mahalarta 334 daga ƙasashe 133.
Mahaifin Maryam, Ibrahim Dan’Azumi, ya halarci taron tare da ita, yayin da Gwamna Inuwa Yahaya da wasu jami’an gwamnatin Gombe suka raka su Abuja.
Da take mayar da martani, Maryam ta gode wa Uwargidan Shugaban ƙasar bisa karramawar, tana mai cewa musabaƙar ta ba ta damar samun ƙwarewa da gogewa a matakin duniya.
Ta ce tana fatan nasarar da ta samu za ta ƙarfafa sauran matasan Nijeriya su ƙara himma wajen neman ilimi da kuma bunƙasa baiwarsu.
Maryam ta kuma yi kira ga matasa da su kula da ci gaban kansu ta fuskar ilimi, tunani da lafiyar jiki.
