Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani mutum da har yanzu ba a gano ko wanene ba ya mutu bayan wutar lantarki ta kama shi yayin da ake zargin yana ƙoƙarin lalata wata na’urar transfoma domin satar kayayyakin cikinta a yankin Abam-Ama da ke ƙaramar Hukumar Okrika ta Jihar Ribas.
Kwamandan Rundunar Tsaron Fararen Hula (CJTF) ta Okrika, Igwe Godswill, ne ya bayyana hakan ranar Talata, inda ya ce mambobin rundunar ne suka gano lamarin yayin da suke sintiri a yankin.
A cewarsa, an sanar da rundunar da safiyar Talata cewa an gano gawar mutumin a wurin da transfomar take.
Ya ce ana zargin mutumin ya shiga wurin ne da nufin lalata transfomar, amma wutar lantarki ta dawo a lokacin da yake aikin, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Godswill ya ce an kuma samu wasu kayayyakin da ake zargin mutumin ya yi amfani da su wajen aikin, ciki har da wani zanen ƙarfe, tocila da wasu kayan aiki.
Ya ce an kai rahoton lamarin ga Rundunar ’Yan Sandan Okrika domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamandan ya yi kira ga matasa da sauran mazauna yankin da su guji satar kayayyaki da lalata kadarorin gwamnati, tare da neman hanyoyin halal na samun abin dogaro da kai.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko abin da suke zargi.
Godswill ya ce har yanzu ba a gano mutumin da ya mutu ba, yana mai cewa wasu daga cikin mutanen da ake zargin suna aikata irin waɗannan laifuka kan zo daga wurare masu nisa.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ba ta fitar da wani bayani kan lamarin ba.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Agabe Blessing Kaborlo, ba ta amsa kiran waya ko saƙon neman bayani da aka aika mata kan lamarin ba.
