Mulki zai dawo Arewa bayan wa’adin Tinubu biyu — Zulum

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce shugabannin Arewa sun amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake samun wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa fahimtar cewa bayan kammala wa’adinsa biyu, shugabancin ƙasar zai koma yankin Arewa.

Zulum ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kaduna, yayin da yake jawabi bayan wata ganawa da ƙungiyar mata malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar Arewa da sauran sassan ƙasar.

Gwamnan ya bukaci ’yan Nijeriya su yi haƙuri tare da ci gaba da bai wa Gwamnatin Tarayya goyon baya wajen ƙoƙarin magance matsalolin tsaro, talauci da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce Arewa ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin Tinubu ya zama shugaban ƙasa, don haka ya kamata a ci gaba da mutunta fahimtar siyasar da aka cimma tsakanin yankin Arewa da Kudancin Nijeriya.

“Kimanin shekaru biyar da suka wuce, mun yanke shawarar tabbatar da haɗin kan Arewa, kuma mun cimma wannan buri,” inji Zulum.

Ya ce shugabannin Arewa sun kuduri aniyar cika alkawuran da suka yi wa takwarorinsu na Kudu dangane da tsarin karɓa-karɓar shugabanci tsakanin yankunan ƙasar.

Zulum ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya su ci gaba da mara wa gwamnatin Tinubu baya domin ba ta damar kammala manufofi da shirye-shiryenta.

Gwamnan ya ce a wata ganawa da wasu fitattun shugabannin Arewa, an tattauna matsalolin tsaro, yara marasa zuwa makaranta da kuma talauci da ke addabar yankin.

A cewarsa, an cimma wasu muhimman matsaya kan hanyoyin magance waɗannan matsaloli da kuma inganta rayuwar al’ummar Arewa.

Zulum ya ce manufar ganawar da mata malaman addinin Musulunci ita ce ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna a faɗin Nijeriya.

Ya bukaci matan da su isar da saƙonnin da aka tattauna zuwa jihohi da al’ummomin da suka fito, domin taimakawa wajen yaɗa zaman lafiya.

Ya ce mata na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya saboda irin tasirin da suke da shi a cikin iyalai da al’ummomi.

“Mata ya kamata a ba su damar tarbiyyantar da ’ya’yansu yadda za su rayu cikin zaman lafiya,” inji shi, yana mai cewa zaman lafiya shi ne babban burin al’ummar Arewa, inda al’ummar yankin ke ci gaba da addu’ar kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Gwamnan ya bukaci mata su yi haƙuri, yana mai cewa koyarwar Musulunci ta tabbatar da muhimmancin haƙuri a lokacin da ake fuskantar jarabawa.

“Idan Allah ya jarrabe mu da wata musiba, wajibi ne mu yi haƙuri kafin sauƙi ya zo,” inji Zulum, yana mai bayyana cewa bai kamata siyasa ta zama sanadin lalata zaman lafiya da zaman tare ba.

Ya tunatar da cewa a baya shugabannin Arewa sun goyi bayan Kudancin Nijeriya bayan sun amfana da mulkin siyasa, inda suka taɓa cimma yarjejeniya da takwarorinsu na Kudu kan fahimtar juna, taimakon juna da kuma tsarin karɓar mulki tsakanin yankunan.

Ya buƙaci Arewa ta yi haƙuri ta bari Kudu ta kammala wa’adin mulkinta, sannan a haɗa kai wajen tsara makomar siyasar yankin.

“Abin da nake faɗa daga zuciyata yake, ba don tsoron kowa ba, sai don Allah,” inji shi.

Gwamnan ya ce yana da yaƙinin cewa adalci zai yi nasara, yana kuma kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai wajen magance matsalolin da ke buƙatar gyara.

Ya yaba wa waɗanda suka shirya taron mata malaman addinin Musulunci, yana mai cewa irin wannan zama na da muhimmanci wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Ya kuma buƙaci mahalarta taron su shirya makamantan taruka a jihohinsu, musamman domin haɗa kan mata wajen tabbatar da zaman tare cikin lumana.

Zulum ya bayyana cewa mata na da kaso mai tsoka na kuri’un da ake kaɗawa a Jihar Borno, inda ya kiyasta cewa suna da kusan kashi 60 zuwa 65 cikin 100 na kuri’un da ake kaɗawa.

Saboda haka, ya jaddada muhimmancin sanya mata cikin shirye-shiryen da suka shafi zaman lafiya, haɗin kai da kuma shiga harkokin siyasa cikin gaskiya da sanin ya kamata.

By ukarofi

Leave a Reply