Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masana’antar Harkokin Ruwa ta Nijeriya na shirin samun sabon ci gaba a fannin jigilar kayayyaki da kasuwancin ƙasa da ƙasa, bayan gwamnatin Amurka ta ɗage wani takunkumin tsaro da ta shafe tsawon shekaru 12 tana ƙaƙaba wa jiragen ruwa masu tutar Nijeriya da ke zuwa tashoshin jiragen ruwa na Amurka.
Ana sa ran matakin zai rage wasu ƙarin kuɗaɗen tsaro da kuma matakan gudanarwa da a baya ake buƙatar masu jiragen ruwa su bi yayin zirga-zirga tsakanin Nijeriya da Amurka.
Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Harkokin Afirka, Frank W. Garcia Jr., ne ya bayyana matakin a cikin wata wasiƙa da ya aikewa Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola.
Garcia ya ce ɗage takunkumin zai kawo wa masu harkar sufuri ta ruwa alfanu kai tsaye, musamman ta hanyar rage kuɗaɗen da suke kashewa kan matakan tsaro, tare da rage lokacin da jiragen ruwa ke ɗauka a tashoshin jiragen ruwa da kuma inganta sahihancin jadawalin zirga-zirgarsu.
A cewar Garcia, matakin ya biyo bayan ci gaba da samun ingantaccen tsaro a tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya, da kuma yadda ƙasar ke ƙara bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na yaƙi da ta’addanci.
Takunkumin da aka ƙaƙaba a baya ya sanya jiragen ruwa masu tutar Nijeriya da ke shiga tashoshin jiragen ruwa na Amurka fuskantar ƙarin buƙatun tsaro na tsawon fiye da shekaru goma.
Matakan sun kasance suna ƙara kuɗaɗen gudanar da harkokin sufuri tare da kawo tsaiko ga ingancin kasuwancin harkokin ruwa tsakanin Nijeriya da Amurka.
Yanzu da aka ɗage takunkumin, ana sa ran masu jigilar kayayyaki ta ruwa daga Nijeriya za su fuskanci ƙarancin matakan takardu da sauran ƙa’idojin da suka kasance suna jinkirta ayyukansu yayin isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka.
Hakan na iya kuma ƙara wa tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya jan hankali a idon manyan kamfanonin jigilar kayayyaki na ƙasa da ƙasa da ke neman hanyoyin kasuwanci masu sauƙin gudanarwa da riba, musamman ganin cewa raguwar kuɗaɗen tsaro na iya taimakawa wajen rage yawan kuɗin gudanar da ayyukan su.
Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ya ce ɗage takunkumin zai ƙara wa Nijeriya ƙarfi a kasuwar harkokin ruwa ta duniya.
Oyetola ya ce rage kuɗaɗen tsaro, tare da saurin sauke kaya da ɗaukar wasu kayayyaki daga jiragen ruwa, na iya ƙara wa tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya gasa da sauran tashoshin duniya, tare da taimakawa wajen cimma burin gwamnatin ƙasar na bunƙasa harkokin ruwa da tattalin arzikin da ke dogaro da albarkatun teku.
Ministan ya danganta wannan ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ba da muhimmanci ga harkokin ruwa da tattalin arzikin teku, da kuma ƙara inganta tsaron ruwan Nijeriya da bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
Saboda haka, ana sa ran ɗage takunkumin zai wuce amfaninsa ga kamfanonin jigilar kayayyaki kaɗai, domin zai iya samar da fa’ida ga ɗaukacin masana’antar harkokin ruwa da kuma ƙara inganta alaƙar kasuwanci tsakanin Nijeriya da Amurka.
Wannan gagarumin ci gaba ya biyo bayan shekaru na haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa da Tsaron Teku ta Nijeriya (NIMASA) da Rundunar Tsaron Tekun Amurka.
Hukumomin biyu sun shafe shekaru suna aiki tare kan batutuwan tsaron teku da bin ƙa’idoji, yayin da Nijeriya ke ƙoƙarin ƙara inganta ƙa’idojin tsaro da suka shafi jiragen ruwa masu amfani da tutarta.
ɗage takunkumin na wakiltar wani muhimmin ci gaba a wannan yunƙuri, kuma ana sa ran zai ƙara ƙarfafa hɗin gwiwa tsakanin hukumomin harkokin ruwa na Nijeriya da takwarorinsu na Amurka.
Ana sa ran Gwamnatin Tarayya za ta yi amfani da wannan ci gaba wajen ƙara zurfafa haɗin gwiwar Nijeriya da Amurka a harkokin ruwa, tare da ɗaukar matakan da za su jawo hankalin ƙarin kamfanonin jigilar kayayyaki na ƙasa da ƙasa zuwa tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya.
Haka kuma, gwamnati na iya amfani da wannan sabon matsayi na Nijeriya a fannin tsaro wajen ƙara bunƙasa rawar da ƙasar ke takawa a harkokin kasuwancin ruwa na duniya, da kuma cimma manufofinta na bunƙasa harkokin ruwa da tattalin arziƙin da ya shafi albarkatun teku.
