
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta wallafa sunaye da bayanai akan ‘yan takarar shugaban ƙasa guda 19 da abokan tafiyarsu daga jam’iyyu daban-daban domin karawa a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe, matakin da ya bayar da dama a gare su su fara yawon yaƙin neman zaɓe a ranar 19 ga Agusta.
Wannan mataki wani ɓangare ne na biyayya ga Sashe ma 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya hukunta wa hukumar ta wallafa sunayen ‘yan takara da suka ƙunshi bayanai na kai-tsaye akansu.
Hakan zai ba wa al’umma damar yin nazari akan bincika da tabbatar da sahihancin bayanan da ‘yan takarar suka bayar domin shiga zaɓen.
A cewar jaddawalin sunayen, Shugaba Bola Tinubu ne ɗan takarar da jam’iyya mai mulki (APC) ta fitar a matsayin ɗan takara tare da Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar shi ne na ADC da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin abokin tafiyarsa.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambara, Peter Obi kuwa, ya tsaya ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NDC tare da tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin abokin tafiya.
Ga cikakken jaddawalin ‘yan takarar kamar yadda NewsPointNigeria ta wallafa:
“Bola Tinubu – All Progressives Congress (APC)
Atiku Abubakar – African Democratic Congress (ADC)
Peter Obi – Nigeria Democratic Congress (NDC)
Senator Sandy Onor – Peoples Democratic Party (PDP)
Omoyele Sowore – African Action Congress (AAC)
Donald Duke – Peoples Redemption Party (PRP)
Okwori Ada Elizabeth Frederick – National Democratic Party (NDP)
Chukwu Anita Zugwai – Young Progressives Party (YPP)
Rufai Adekunle Omoaje – Action Alliance (AA)
Adenuga Sunday – Boot Party
Memeh Samuel – Democratic Liberty Alliance (DLA)
Nwanyanwu Daniel Danerechukwu – Zenith Labour Party (ZLP)
Okereke Sunday Chibuzor – Labour Party (LP)
Okereke Iken Esther – National Rescue Movement (NRM)
Abbas-Bin Aliyu – Action Democratic Party (ADP)
Dikwa Suleiman Mohammed – New Nigeria Peoples Party (NNPP)
Adebayo Adewole Ebenezer – Social Democratic Party (SDP)
Seyi Makinde – Allied Peoples Movement (APM)
Yusuf Kabiru – Action Peoples Party (APP).”
Haka kuma, jaridar ta wallafa na abokan tafiyar ‘yan takarar kamar haka:
“Kashim Shettima (APC)
Rotimi Amaechi (ADC)
Rabiu Kwankwaso (NDC)
Shehu Hussaini (AA)
Egbeola Olawale Mertins (YPP)
Ike Chinazam (ADP)
Mustapha Usman Turaki (Boot Party)
Balogun Alex (DLA)
Chikwuemeka Uchenna Anthony (NDP)
Magashi Haruna Garba (AAC)
Umaru Babangida (PDP)
Konto Hajja Bintu (LP)
Hassan Khalid (ZLP)
Samuel Magdalene Gali (NRM)
Abubakar Isah (NNPP)
Buba Musa (PRP)
Bugaje Usman Mohammed (SDP)
Ibrahim Adamu Bala (APM)
Ofordile Peace Egobia (APP).”
A cewar takardun da aka miƙa wa INEC, an haifi Tinubu ne a ranar 29 ga Maris, 1952.
Ya ce, yana da digirin farko a a fannin Kasuwanci a Jami’ar Chicago a 1979. Ya kuma ce kuma ya yi hidimar ƙasa a tsakanin Disambar 1982 da Nuwamban 1983. Saidai takardar ba ta ƙunshi batun iliminsa na firamare da sakandare ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya nuna cewa ya halarci Lamisula I Primary School tsakanin 1972 da 1978 gabanin samun takardar WAEC a Government Secondary School, Potiskum a 1983.
Haka kuma ya yi digirin farko a tsangayar noma a Jami’ar Maiduguri da mafi kaywun daraja na biyu a 1989, sannan daga bisani ya yi digiri na biyu a tsangayar tattalin noma a Jami’ar Ibadan.
Atiku ya samu shaidar kammala karatu ta farko ne a 1954 sai kuma ta WAEC a 1961. Haka kuma ya ce ya yi digirin digir a tsangayar hulɗar ƙasa-da-ƙasa daga Jami’ar Anglia Ruskin a 2020.
shi kuwa Amaechi, an haife shi ne a ranar 27 ga Mayu, 1965, a Ubima, da ke Ƙaramar Hukumar Ikwerre ta Jihar Ribas. Ya harci makarantar St. Theresa’s Primary School da 1970 zuwa 1976 kuma ya yi WAEC a Government Secondary School, Okolobiri, a 1982.
Ya kuma yi digirin farko a tsangayar Turanci da Adabi daga Jami’ar Fatakwal a 1987, inda kuma ya shugabanci ɗalibai da wasu karance-karance a fannim shari’ar daga Jami’ar Baze da Makarantar Horar da Lauyoyi ta Ƙasa da kuma King’s College da ke London.
