Trump ya dakatar CNN da wasu manyan gidajen jarida a Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da gaggauta dakatar da wasu manyan kafafen yaɗa labarai na ƙasar daga gudanar da harkokinsu a Fadar White House sakamakon zargin su da wallafa “ƙirƙira da ƙarairayi” akan gwamnatinsa. Gidajen jaridar sune CNN, MSNOW da kuma Politico.

Trump ya bayyana haka ne a ranar Juma’a ta dandalinsa na Truth Social, inda ya ce matakin zai fara aiki ne a nan take, yana mai gargaɗin sauran kafafen labarai ka iya fuskantar irin matakin.

Haka kuma, shugaban ya zargi kafafen da wallafawa da yaɗa labaran da ya ɗauke su a matsayin ƙarya akan gwamnatinsa, karan kansa da kuma gwamnatin Amurka.

Wannan sanarwa da Trump ya yi ba ta bayar da bayanan yadda fadar shugaban ƙasar take shirin aiwatar da hukuncin ba ko kuma matakin takunkumin da aka sanya wa gidajen yaɗa labaran.

Haka kuma, ba a gano ko matakin ya shafi ‘yan jaridar kafafen ba da ka aiki a fadar ko iyakance harkokin da za su riƙa ruwaitowa. Wannan mataki dai yana wakiltar wani ɓangare na rikicin tsawon lokaci tsakanin Donald Trump da wasu gidajen a yaɗa labaran Amurka.

By Babaji

Leave a Reply