Matar babban jami’in kuɗin ISWAP da ɗansu sun miƙa wuya ga sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce matar babban jami’in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP tare da ɗanta mai shekara 11 sun miƙa wuya ga dakarunta na Atisayen Haɗin Kai a ƙauyen Kusuma da ke Jihar Borno a Shiyyar Arewa maso Gabashin ƙasar.

Sojojin ta bakin jami’in yaɗa labaran dakarun na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, sun ce bincike ya nuna cewa mijin matar, wanda ya kasance babban kwamandan ISWAP ne, ya miƙa wuya a ranar 25 ga Yuli kuma shi ne ya wanda ya umarce ta da ta fito daga maɓoyarsu tare da ɗansu.

Ya bayyana cewa, tuni aka gudanar da aikin tantance matar da ɗan nasu kuma ana cigaba ɗaukar bayanai da gudanar da bincike akansu bisa tsarin doka.

Hakan na zuwa ne bayan da dakarun tsaron suka ƙaddamar da wasu atisaye daban-daban da suka yi sanadiyyar kama mutum shida da ake zargin masu alaƙa ne da mayaƙan ISWAP tare da kwato wasu kayayyaki a Borno

Bincike ya nuna cewa, ana zargin mutanen ne da samar wa ƙungiyar ISWAP kuɗin shiga ta hanyar saye da sayarwa a kasuwannin dabbobi da ke Gubio, Damasak da kuma Ajuwango.

Sanarwar ta ƙara da cewa, mayaƙan sun tsere a wani samame ta daban da sojojin suka kai a yankin Turoh bayan samun bayanan sirri.

Bayan bincike a yankin, dakarun sun ƙwato babura biyu da kuma tarin miyagun ƙwayoyi da mayaƙan suka bari a baya, yayin da rundunar ta ce za ta cigaba da ƙarfafa hare-haren da suka dogara da sahihan bayanan sirri.

By Babaji

Leave a Reply