Yadda aka samu sarƙaƙiya kan dalilan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a hannun Sibil Difens

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Abin da ya fara daga atisayen ƙoƙarin tabbatar da kiyaye doka da oda kan harkar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Minnan Jihar Neja, ya koma abin alhini sakamakon mutuwar matasa masu haƙar ma’adinai guda 37 a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC).

Wannan al’amari ya janyo zanga-zanga, mabambanta bincike a hukumance, dakatarwa da umarnin shugaban ƙasa da kuma kiraye-kiraye na a tabbatar da adalci daga ɓangaren al’umma.

Yayin da aka shiga halin bincike kan gano ainihin yadda al’amarin ya kasance, abubuwa da dama sun bayyana kama daga kama masu haƙar ma’adinan, dalilan mutuwarsu da abin da aka gano a Babban Asibitin Minna.

Wannan al’amarin ya haifar da tambayoyi masu tsauri kan halin da aka tsare matasan, halin ofishin, adadin waɗanda aka tsare a gurin, matakin kulawar da aka ba su, abin da ya faru a daren faruwar mace-macen da kuma ko akwai sakaci, cikowa, rashin wadataccen iska domin samun numfashi, guba, cuta ko wani dalili da ya sabbaba aukuwar lamarin.

A yanzu dai babu wani dalili da za ce shi ne ainihin abin da ya sabbaba mutuwarsu a hukumance. Da fari dai NSCDC ta yi iƙirarin cewa al’amarin ya auku ne sakamakon ɓarkewar wata cuta, yayin da hedikwatarta ta ƙasa ta ƙalubalanci yanke hukunci haka ba tare da an kammala binciken gawa ba daga ɓangaren likitoci. Saidai, an fitar da wasu bayanai masu tayar da hankali daga waɗanda suka tsira, ‘yan uwa, jami’an asibiti da hukumomin gwamnati, waɗanda sun faɗaɗa adadin tambayoyin da ake da su kan abin alhinin.

Ita kuwa NSCDC reshen Jihar Neja, cewa ta yi jami’ansu sun ƙaddamar da “atisayen fallasa” a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankunan M.I. Wushishi Estate da ƙauyen Lokoto da ke Minna, kamar yadda Kwamandanta, Suberu Aniviye ya bayyana, inda ya ƙara da cewa sun kama mutane da dama da suke aikin haƙar ma’adinai ba bisa doka ba. Daga bisani a safiyar ranar Alhamis, ta ce an samu wasu daga cikinsu sun rasu sakamakon abin da ta kira da ɓarkewar wata cuta. Saidai ba ta bayar da ƙarin bayani kan yadda al’amarin ya faru ba.

Bayan haka ne aka samu ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira da ya nemi a sakaye sunansa, wanda ya ce an fesa wa takwarorin nasa ne wani sinadari yayin da suke cikin ɗakin ajiye mai laifi. Ya bayyana haka ne a lokacin da Gwamna Umaru Bago na jihar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo suka gana da shi tare da wasu biyu da suka tsira don jin abin da ya faru. Ya ce, su 67 ne jami’an NSCDC suka jibge a wani ɗaki. A cewarsa, matasan sun yi ta yin magiya ga jami’an na Sibil Difens cewa zafi ya dame su kuma suna buƙatar su sha wani abu, amma aka yi buris da su. Sannan ba a ba su ruwa ba kuma an hana iyalansu su kai musu ruwa ko abinci.

A nasa ɓangaren, Gwamna Bago ya ce abin da aka gano a asibitin da gidan ajiyar gawa sun ƙara haifar da waɗansu tambayoyi. A cewarsa, an ga wasu gawarwakin da kumfa a bakunansu da tartsatsin jini a jikkunansu yayin da kuma aka ga fatar wasu daga cikinsu ta fara ɗayewa. Gwamnan ya kuma caccaki Aniviye da sauran jami’an da ke bakin aiki kan abin da ya kira da rashin “imani” wajen jibge mutane masu yawa a irin wannan guri na tsawon sama da sa’o’i 24.

By Babaji

Leave a Reply