Shugabanci na gari ‘yan ƙasa suke so ba gina gadoji ba – Tinubu ga gwamnoni

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya kirayi gwamnonin jihohi da su daina gina gadar sama a jihohinsu, a madadin haka su mayar da hankali wajen sarrafa kuɗaɗen da aka ware musu na tarayya zuwa bunƙasa hanyoyin sadarwa da hanyoyi da za su inganta yanayin rayuwa da cigaba al’umma da jihohinsu.

Tinubu ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar sarakunan gargajiya daga Jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Olubadan na Masarautar Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, waɗanda suka je domin taya shi murna kan nasarar ceto ɗalibai da malaman makaranta da aka sace a Karamar Hukumar Oriire bayan kwana 56 a hannunsu.

Shugaban kasar, wanda ya yi jawabi ga Ladoja da sauran wadanda suka taba yin aiki a matsayin gwamnoni, ya ce, “Kudin aikin ya yi yawa. Amma kudin da nake turawa zuwa jihohi, da ace kuna da shi a lokacin ku, ko a lokacin da nake, da ya bambanta.

Ya kara da Cewa “Suna karbar kudinsu sau hudu zuwa biyar. Babu wanda ke karbar bashin albashi yanzu. Masu fansho suna karbar albashinsu.

“Ya kamata su yi fiye da haka maimakon gina gine-gine marasa Amfani na Gadoji a inda babu zirga-zirgar ababen hawa,gina hanyoyi da hanyoyin sadarwa don inganta rayuwar jama’a da kuma baiwa hukumomin tsaro dama da tallafi don shiga yankunan da ake fama da matsalolin tsaro ya fi wadannan ayyukan marasa amfani.

By Babaji

Leave a Reply