Jaddawalin shirye-shiryen jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari

Spread the love

1-An ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu a Najeriya don makokin Marigayin

2-An kafa Kwamitin Manyan Jami’an gwamnati don tsara jana’izar girmamawa ga tsohon shugaba Buhari wanda sakataren gwamnatin tarayya Sen. George Akume zai jagoranta.

3-An ɗage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa daga gobe zuwa juma’a don zaman makoki

4 An umarci mambobi 25 na Majalisar Zartarwar da su wuce Daura don halartar jana’izar zaman makoki na kwanaki uku

4-An ayyana kwanaki 7 na zaman makoki a ilahirin Najeriya tare da yin ƙasa-ƙasa da tutar ƙasar

5- Babbar tawaga ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kasa na can na kammala shirye-shiryen kawo gawar da iyalan mamacin gida

6- Za a yi takaitaccen faretin sojoji a filin jirgin sama na jihar Katsina don tarbar gawar.

7- Za a yi sallar jana’iza da rufe gawar a Daura.

8 An buɗe shafin karɓar ta’aziyya a dukkan ma’aikatun gwamnatin tarayya, da na hukumomi, da ilahirin ofisoshin jakadanci na Najeriya dake ƙasashen waje.

9- Ana sa ran isowar gawar Katsina da ƙarfe 12 na rana a ranar Talata.

10- Za a yi jana’izar a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025.

10- Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai karɓi gawar tsohon shugaban kasa a Katsina tare da manyan baƙi.

By Babaji