
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasarar sulhunta rikicin da ke tsakanin ‘ya’yan Gamayyar Ƙungiyoyi Huɗu na Kansilolin APC ta Ƙasa ta ‘Four Nigerian APC Councilors’ Forum’ bayan tsawon lokaci.
Bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi umarnin shiga tsakani, Ganduje ya cimma haka ne ta hanyar zama da wakilan ƙungiyar, wadda akan haka ne ta gudanar da zama a ranar Alhamis, 29 ga Yuli, 2026 tare da fitar da sababbin matakan gudanarwa.
A yayin haka ne ta cimma matsayar naɗa tsohon shugaban APCn a matsayin Uban Ƙungiya bisa ƙoƙarinsa wajen ganin rikicin da ke tsakanin mambobin ƙungiyar ya zo ƙarshe, lamarin da ya sa ta karrama shi da naɗin.
Haka kuma, ƙungiyoyin Progressive Serving Councilors’ Forum of Nigeria, Coalition of Past and Present Councilors of Nigeria for Tinubu/Shettima 2027, National Progressives Councilors Forum da kuma National Association of Past and Present Progressives Councilors sun amince da zama ƙungiya guda bisa umarnin Ganduje.
Ƙungiyar ta samar da National Progressive Serving Councilors Forum a matsayin ƙungiyar kansiloli masu ci na jam’iyyar ta ƙasa. Sai kuma National Progressives Former Councilors Forum a matsayin ta tsofaffin kansilolin APC.
Sannan, gamayyar ƙungiyoyin ta amince da kafa kwamitin riƙo da zai jagoranci harkokin ƙungiyar, wanda zai tabbata da amincewar kwamitin amintattu da kuma uban ƙungiyar.
Kazalika, mambobin sun amince da kafa kwamitin amintattun ƙungiya (BoT), wanda zai yi aikin kula da harkokin ƙungiyoyin biyu ta yadda zai tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya acikin ‘ya’yan ƙungiyoyin biyu.
Har ila yau, ta amince da Hon. Muslihu Yusuf, wanda shi ne shugaban ƙungiyar na farko a matsayin shugaban kwamitin amintattun, sannan Hon. Barista Muhammad Abubakar Shehu a matsayin Darakta-Janar na ƙungiyar.
