Gwamnatin Gombe ta amince da haɗin gwiwa da BREACH kan ranar matasa ta duniya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta bayyana shirinta na yin haɗin gwiwa da ƙungiyar BREACH Initiative for Leadership Development domin tabbatar da nasarar gudanar da bikin ranar matasa ta duniya ta 2026, wanda aka tsara domin ƙarfafa shugabancin matasa, wayar da kan jama’a game da alhakin ɗan ƙasa da kuma bunƙasa tsaro.

An bayyana hakan ne yayin ziyarar neman haɗin gwiwa da ƙungiyar ta kai wa wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Hon. Adamu Dishi Kupto; Kwamishinan Matasa da Wasanni, Hon. Yusuf Abdu Kwadom; Mai Kula da Aikin NEWMAP-EIB, Dr. Shitu Whanda; da Shugabar Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Gombe (GIRS), Hajiya Aishatu Adamu Yaro.

Jagoran tawagar, kuma shugaban ƙungiyar BREACH, Comrade Abdul’azeez Sani Labaran, ne ya jagoranci ziyarar tare da Abubakar Waziri na Access Initiative, Yasir Aliyu Dala na FOYEA da sauran wakilan ƙungiyoyin haɗin gwiwa.

A yayin ziyarorin, tawagar ta nemi haɗin gwiwa daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati domin shirye-shiryen bikin ranar matasa ta duniya da za a gudanar ranar 12 ga Agusta, 2026.

Har ila yau, ƙungiyar ta bayyana shirinta na gudanar da wani babban shiri mai sassa uku ƙarƙashin taken “ƙarfafa matasa domin shugabanci mai ɗorewa da gina ƙasa

A cewar masu shirya taron, shirin zai haɗa da fareti na ƙungiyoyin tsaro na sa-kai daga Fadar Sarkin Gombe, tattakin wayar da kan jama’a zuwa Gidan Gwamnati, da kuma liyafa tare da bayar da lambobin yabo ga fitattun matasa.

Da yake jawabi yayin ziyarorin, Labaran ya ce manufar shirin ita ce ƙara wa matasa damar taka rawa wajen gina ƙasa, bunƙasa shugabanci nagari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin matasa da hukumomin gwamnati.

Jami’an gwamnatin da tawagar ta ziyarta sun yaba da wannan yunƙuri tare da ba da tabbacin cewa gwamnati za ta mara masa baya, suna mai bayyana shi a matsayin wani shiri da ya dace da ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa matasa da inganta zaman lafiya da tsaro.

Sun ƙara da cewa shirin zai ba matasa damar nuna basirarsu, ƙwarewarsu da irin baiwar shugabanci da suke da ita, tare da tallafa wa manufofin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na bunƙasa matasa da samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply