Buhari: Ribaɗu da Janar Musa za su jagorancin kwamitin Tinubu na makokin ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa kwamitin ministoci don shirya zaman makoki na ƙasa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu, wanda ya rasu a ranar 13 ga watan Yuli a wani asibitin Landan.

An kafa kwamitin ne a ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda zai yi aikin tsara yadda za a gudanar da zaman makokin don karrama marigayin.

A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren, Segun Imohiosen ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin karrama kyawawan ayyukan Buhari da mutuntawa musamman a mataki na ƙasa.

Kwamitin ya ƙunshi manyan jami’an gwamnati da jagororin hukumomin tsaro. Ga jaddawalinsu kamar yadda News Point Nigeria ta wallafa:
“Honourable Minister of Finance and Coordinating Minister of the Economy
Honourable Minister of Budget and Economic Planning
Honourable Minister of Defence
Honourable Minister of Information and National Orientation
Honourable Minister of Works
Honourable Minister of Interior
Honourable Minister of the Federal Capital Territory (FCT)
Honourable Minister of Housing and Urban Development
Minister of State for Health and Social Welfare
Honourable Minister of Art, Culture and Creative Economy
National Security Adviser
Special Adviser to the President on Policy and Coordination
Senior Special Assistant to the President on Political and Other Matters
Inspector General of Police
Director-General of the Department of State Services (DSS)
Chief of Defence Staff.”

Haka kuma, Tinubu ya umarci baki ɗaya ma’aikatu da hukumomi da su buɗe rajistar miƙa ta’aziyya ga rashin tsohon shugaban a kowace mashiga ta ofisoshinsu domin bai wa al’umma damar karrama shi a karo na ƙarshe.

By Babaji