
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta zaɓi ranar Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin karrama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani ta fitar, ta ce hutun wani ɓangare ne na jimamin mako guda da Shugaba Bola Tinubu ya sanar.
Ta kuma ce, Ministan Ma’aikatar, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, biyo bayan amincewar Shugaba Tinubu akan haka.
Ya ce, hakan karramawa ce ga tsohon shugaban ƙasar bisa gudunmuwarsa ga harkar dimukraɗiyya a Nijeriya da samar wa ƙasa ci-gaba a ƙarƙashin mulkinsa da ma wasu lokuta.
Kazalika, ya kirayi al’umma da su yi amfani da ranar wajen girmama halin marigayin na ƙoƙarin samar da ci-gaban zaman lafiya, kishin ƙasa da haɗin kanta domin tabbatar da nasara a gare ta ta fannoni da dama.
